Wasu masu binciken fasaha na kasar Sin, sun cimma sabon sakamako a fannin saurin sadarwa tsakanin tauraron dan adam da doron duniya, inda suka karya matsayin saurin da ake da shi a baya, ta amfani da salon X-band mai tasha guda.
Rahotanni na cewa masu binciken, daga cibiyar binciken harkokin sadarwar samaniya ko AIR, karkashin hukumar lura da binciken kimiyya ta kasar Sin, sun cimma nasarar gudanar da sadarwa da saurin da ya kai megabit 2,100 duk dakika, adadin da ya haura wanda ake iya samu ta fasahar “microwave”, da karin kaso 75 bisa dari na saurin sadarwar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














