• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Karrama Dalibar Kaduna Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar Karatun Alkur’ani Ta Duniya

byShehu Yahaya
4 months ago
Kaduna

Kwamitin shirya musabakar gasar karatun alkur’ani na karamar hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna ya karrama daliba ‘yar asalin Jihar Kaduna, wacce ta zo ta biyu a gasar karatun alkurani ta duniya.

Daliba mai suna Khadija Tahir Umar, ta kasance ‘yar asalin karamar hukumar Igabi, an ba ta lambar yabon ne bisa jajircewa wajen ganin Jihar Kaduna ta zo ta biyu a a gasar ta duniya.

  • Wakilin Sin Ya Soki Yadda Amurka Ke Tafiyar Da Kudurin Takunkuman Sudan Ta Kudu
  • Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB

Da yake mika mata lambar yabon, garkuwan musabakar karatun alkurani na Jihar Kaduna, Honarabil Yusuf Ibrahim Zailani ya jinjina wa kokarin dalibar wajen tabbatar da ganin ta daga darajar Jihar Kaduna a idon duniya.

Zailani, wanda shi ne dan majalisar dokokiin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar karamar hukumar Igabi ta Yamma a majalisar dokokin jihar, ya bukaci iyaye da su kara kulawa wajen tarbiyyar da ‘ya’yansu da kuma ba su ilimin addini.

“Ba ku ga yadda wannan dakibar ta fito da darajar karamar hukumar Igabi da Jihar Kaduna a idon duniya ba. Na ba ta kyauta naira miliyan daya, mahaifiyarta da ta kula da ita na ba ta kyauta naira dubu dari hudu, shi Kuma mahaifinta na ba shi kyauta naira dubu dari shida, na ba da wannan kyautar ne domin nuna jin dadina na samun labarin Jihar Kaduna ta zo ta biyu a duniya,” in ji Zailani.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya.

Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu.

Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Next Post
Gwamna Dikko Zai Sake Tsarin Babbar Kasuwar Jihar Katsina

Majalisar Dokokin Katsina Ta Ayyana Gwamna Radda A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A 2027

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version