Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 6, da Litinin, 9 ga watan Yuni, 2025, a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Sallar Layya ta bana.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar Dr Magdalene Ajani ta fitar ranar Litinin a Abuja.
Yayin da yake taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar wannan rana, ya yi kira gare su da su ci gaba da yin koyi da sadaukarwa da tausayi kamar yadda Annabi Ibrahim (A.S) ya yi, tare da yin amfani da wannan lokaci wajen yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya da wadata.