Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da tallafin Naira Miliyan 337 don gudanar da shagalin sallah ga mata 11, 229 na rumfunan zabe 3,743 a duk fadin kananan hukumomi 21 na jihar. An zabi mata uku ne daga kowace rumfar zabe a mazabu 3,743 da ke a fadin jihar, inda kowace mace zata karbi N30,000 a matsayin tallafi don gudanar da shagalin sallar Eid-kabir.
An gudanar da bikin Kaddamar da bayar da tallafin ne a sakatariyar Jam’iyyar APC da ke Birnin Kebbi a ranar Talata.
- Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya
- Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya
A jawabinsa ga matan da suka ci gajiyar tallafin, Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abubakar Muhammad Kana Zuru, ya ce” wannan tallafin ya zo a lokacin da jama’a ke da bukatar sayen dabbobin layya.
“Bisa ga hakan ne, Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris ya bayar da wannan tallafin don gudanar da shagalin sallar cikin walwala da Jin dadi”.
Shugaban ya gode wa Gwamnan jihar kan wannan kokarin da yayi na tunanin a zakulo mata uku a kowace rumfar zabe a duk mazabun kananan hukumomin 21 na jihar don basu tallafin N30,000 don gudanar da shagalin sallar Eid-kabir, “muna masa godiya a madadin matan da suka ci gajiyar tallafin”.
Daga karshe, Zuru ya yi kira ga sauran shugabanni da su yi koyi da Gwamnatin jihar Kebbi kan tallafa wa al’umma a jihar musamman a irin wannan lokaci ga wannan lokaci da jama’a ke da bukatar yin layya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp