Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya bayar da umarnin gudanar da bukukuwan karamar Sallah saffa-saffa tare da dakatar da Hawan Bariki, Hawan Sallah da sauran bukukuwan Sallah a dukkan masarautun jihar.
Umurnin ya biyo bayan mummunan bala’in ambaliya da ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a Mokwa da kewayenta.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Ambaliyar Garin Mokwa A Neja
- Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sanadin Ambaliya A Neja Ya Karu Zuwa 115
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman a lokacin da yake mika wannan umarni, ya ce an dauki matakin ne a matsayin girmamawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma ba da damar zaman makoki da addu’o’i a gare su.
Da yake mika umarnin Gwamnan ga Masarautun, Sakataren ya bayyana cewa, ambaliyar Mokwa na daya daga cikin mafi munin annoba da ta afku a jihar tsawon shekaru da dama da suka gabata, wacce ta yi sanadin salwantar rayuka da rugujewar gidaje da ababen more rayuwa da dama.