• English
  • Business News
Thursday, June 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Na Yunkurin Rage Dala Biliyan 1.5 Da Ake Kashewa Wajen Shigo Da Madara

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
3 weeks ago
in Labarai
0
Gwamnatin Tarayya Na Yunkurin Rage Dala Biliyan 1.5 Da Ake Kashewa Wajen Shigo Da Madara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yayin da Nijeriya ke bikin ranar madara ta duniya na 2025, gwamnatin tarayya ta sanar da shirin rage sama da dala biliyan 1.5 da kasar ke kashewa a duk shekara daga shigo da madara da kuma bunkasa samar da nonon cikin gida.

Da yake magana a ranar Asabar a Abuja, ministan bunkasa harkokin kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya ce gwamnati na shirin ninka yawan nonon da Nijeriya ke samarwa a duk shekara daga tan 600,000 zuwa ton miliyan 1.2 cikin shekaru biyar masu zuwa.

  • Wani Matashi Dan Shekara 33 Ya Rasu Bayan Ya Fada Wata Tsohuwar Rijiya A Kano
  • Shugabannin Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

Bikin na bana shi ne irinsa na farko tun lokacin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa hukumar kula da kiwon dabbobi na tarayya a watan Yunin 2024, ministan ya ce, taron wata alama ce ta azama da himmar da suke da shi na inganta bangaren kiwo a fadin kasar nan.

“Muna shan akalla madara tan miliyan 1.7 a duk shekara, har yanzu kuma, muna samar da kaso 35 ne kawai na yawan abun da kasar ke bukata. Sauran, kusan na sama da dala biliyan 1.5, shigo da su ake yi, mafi yawanci a launin madaran gari,” Maiha ya shaida.

Ya yi nuni da cewa, yawan madarar da Nijeriya ke amfani da shi ya kai lita 8.7 kacal a kowace shekara, wanda ya yi kasa da yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayar da shawarar lita 210, har ma da na Afirka na lita 40.

Labarai Masu Nasaba

Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara

Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga

Domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya zayyana kokarin da ake yi a karkashin dabarun bunkasa kiwon dabbobi na kasa, wanda ya mayar da hankali kan ginshikai guda 10 da suka hada da bunkasa kimar dabbobi, inganta kiwo, kiwon lafiyar dabbobi, samar da kudi, sauya salon kiwo da karfafawa matasa da mata gwiwa kan dogaro da kai.

Maiha ya yi tunin cewa zuwa yanzu ma’aikatar ta samu cimma wasu nasarori da suka hada da yin rajistar nau’in kiwo guda takwas, “na farko a cikin shekaru 48” da kuma samar da wani shiri na kasa kan albarkatun halittun dabbobi tare da hadin gwiwar FAO.

“Dabbobinmu na cikin gida suna samar da lita 1-2 na madara a kullun, idan aka kwatanta da na waje a karkashin gudanarwa da kuma tsarin kiwon lafiya domin shawo kan wanan gibin, dole ne mu tashi tsaye mu magance wannan matsalar,” ya shaida.

Ministan ya kuma bayyana yadda ake zuba jari a fannin kiwon lafiyar dabbobi, gami da fadada samar da alluran rigakafin a Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Kasa (NBRI) daga allurai miliyan 120 zuwa miliyan 850 a duk shekara. An kuma kaddamar da wani wurin ajiyar alluran rigakafi mai amfani da hasken rana mai karfin awo miliyan 40 a Sheda da ke Abuja da dai sauran nasarori.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sallar Layya: Gwamnan Zamfara Ya Buƙaci Musulmin Su Tuna Da Muhimmancin Sadaukarwa Da Halin Ƙwarai

Next Post

Namibia Za Ta Karfafa Hulda Da Sin Yayin Baje Kolin Cinikayya Da Tattalin Arziki

Related

Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara

2 hours ago
Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga
Labarai

Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga

4 hours ago
Kawayen amarya
Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Ƙwace Iko Da Jagorancin Ƙaramar Hukuma A Katsina

6 hours ago
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna
Labarai

Musayar Wuta Tsakanin Sojoji Da ‘Yan Bindiga Ta Ci Rayuka Da Dama A Jihar Neja

8 hours ago
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Zai Rattaba Hannu Kan Kudirorin Sauya Fasalin Haraji 4 A Yau Alhamis 

10 hours ago
Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC
Labarai

Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC

19 hours ago
Next Post
Namibia Za Ta Karfafa Hulda Da Sin Yayin Baje Kolin Cinikayya Da Tattalin Arziki

Namibia Za Ta Karfafa Hulda Da Sin Yayin Baje Kolin Cinikayya Da Tattalin Arziki

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara

Jami’an Tsaro Sun Kashe Mayaƙan Bello Turji Da Yawa A Zamfara

June 26, 2025
Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga

Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga

June 26, 2025
Kawayen amarya

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Ƙwace Iko Da Jagorancin Ƙaramar Hukuma A Katsina

June 26, 2025
An Damke Basarake Da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Hada Baki Da ‘Yan Bindiga A Kudancin Kaduna

Musayar Wuta Tsakanin Sojoji Da ‘Yan Bindiga Ta Ci Rayuka Da Dama A Jihar Neja

June 26, 2025
Tinubu

Tinubu Zai Rattaba Hannu Kan Kudirorin Sauya Fasalin Haraji 4 A Yau Alhamis 

June 26, 2025
Cristiano Ronaldo Na Shirin Tsawaita Kwantiraginsa A Kungiyar Al-Nassr

Cristiano Ronaldo Na Shirin Tsawaita Kwantiraginsa A Kungiyar Al-Nassr

June 25, 2025
Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC

Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC

June 25, 2025
Shugabannin Sin Da Mozamqiue Sun Mikawa Juna Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya

Shugabannin Sin Da Mozamqiue Sun Mikawa Juna Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya

June 25, 2025
MSS: Neman Sinawa ‘Yan Leken Asiri Da CIA Ta Yi Tamkar Wasan Ban Dariya Ne

MSS: Neman Sinawa ‘Yan Leken Asiri Da CIA Ta Yi Tamkar Wasan Ban Dariya Ne

June 25, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Kano Ta Ayyana Ranar Alhamis Hutu Domin Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci

June 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.