• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 9 A Jigawa

by Sulaiman
5 months ago
Jigawa

LABARAI MASU NASABA

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

Mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kauyen Kyaramma da ke karamar hukumar Ringim a jihar JIgawa.
A cewar rundunar ‘yansandan jihar Jigawa, hatsarin wanda ya afku a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 2 na rana, ya rutsa da wasu motoci kirar Golf 3 saloon guda biyu tare da jikkata wasu da dama.
  • Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban Zangon Noma Da Kiwo Ɗauke Da Kasuwar Duniya A Jihar 
  • Ndume Ya Gargaɗi Tinubu Kan 2027: “An Taɓa Yi Wa Jonathan Irin Wannan”
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Shiisu Adam ya fitar, ya bayyana cewa daya daga cikin motocin mai lamba Kaduna MKA 687 AY, wani mutum mai shekaru 35 dan karamar hukumar Hadejia, Adamu Sunusi ne ke tuka motar zuwa garin Gujungu daga Abuja.
A binciken farko da aka gudanar, Adam ya ce, motocin sun yi taho-mu-gamu ne bayan da motar ta kwace wa dayan direban, lamarin da ya sa dukkanin motocin biyu suka kauce hanya. An dauki matakin gaggawa, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Ringim domin kula da lafiyarsu.
Kwamishinan ‘yansanda, CP A.T. Abdullahi, ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa. Ya kuma bukaci direbobi da su rika bin ka’idojin hanya, su guji wuce gona da iri, sannan su tabbatar da cewa, motocin nasu suna cikakkiyar lafiyar zirga-zirga don gujewa afkuwar hadurra.
Sanarwar ta ce, “A yanzu haka fasinjoji 11 suna karbar magani a asibiti kuma suna samun sauki, ana kokarin gano duk wadanda suka rasu domin tuntubar iyalansu.”
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu
Labarai

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe
Labarai

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra
Labarai

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
Next Post
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025
Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.