Gwamnatin kasar Sin ta fitar da halayen tafiyar tattalin arzikin kasar na watan Mayu a jiya Litinin, alkaluman da suka nuna cewa, a wannan wata yawan kudin sayayyar kayan masarufi ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 573.4, wanda ya karu da kashi 6.4% bisa na makamancin lokacin bara. Dadin dadawa, yawan karuwar darajar masana’antun da suka samu ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokaci na bara, kuma yawan kudin shige da ficen hajoji ya kai wajen dalar Amurka biliyan 528.6, wato ya karu da kashi 2.7% bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu, yawan kayayyakin da aka fitar zuwa ketare ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 315.9, wato ya karu da kashi 6.3%. Duba da wadannan alkaluman tattalin arzikin kasar Sin, kafofin yada labarai na duniya sun bayyana cewa, saurin bunkasar sayayyar kayayyakin masarufi na kasar Sin ya kai matsayin koli a cikin watanni 17 da suka gabata, ya bayyana yadda harkokin cinikin wajen kasar yake juriyar matsalolin da ake fuskanta, har ma wasu alkaluman sun zarce na halin da aka yi hasashe a baya.
To ko mene ne dalilin da ya sa kasar Sin ta samu irin wannan ci gaba, duk da cewa muhimman hukumomin tattalin arzikin duniya sun daidaita hasashen da suka yi game da bunkasuwar tattalin arzikin duniya a wannan shekara, duba da yadda ra’ayin nuna bangaranci, da na kashin kai suna kunno kai?
Farfesa jami’ar Renmin ta Sin Wang Xiaosong ya nuna cewa, a watan da ya gabata, an samu ci gaba mai armashi da kai ga matsayi na daya a gun taron tattaunawa na Geneva game da tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Amurka, matakin da zai kyautata huldar kasashen biyu a wannan bangare, har ma ya ciyar da bunsuwar tattalin arzikin duniya gaba. A wani bangare na daban, a cikin gidan kasar Sin, ana da nagartaccen halin bunkasar tattalin arziki, da kasuwa mai girma, da boyayyen karfi mai inganci, dalilin da ya sa Sin ke iya habaka bukatunta na cikin gida, da boyayyen karfin kasuwanninta na gida a lokacin da bukatu a waje ta tsuke. A sa’i daya kuma, mabambantan sana’o’in Sin suna kokarin kyautata hanyoyin da za su bi, duba da bunkasar karfinsu na kimiyya da fasaha, inda karfin takararsu ke kara habaka, matakin da ya ingiza ingantaccen ci gaban tattalin arzikin Sin. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp