An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su iya amincewa da ita har abada.
Ana iya sa ran cewa, hadin gwiwar da Sin za ta yi da tsakiyar Asiya ba wai kawai za ta inganta manyan ayyukan hadin gwiwa ba ne, har ma za ta kara karfafa kokarin “neman sabbin abubuwa masu dadi” da “sabbin kirkire-kirkire”, da sa kaimi ga kasashen shida wajen cimma zamanantarwa tare da juna.
Shugabannin kasashe biyar na yankin tsakiyar Asiya sun nuna goyon baya sosai ga tunanin kasar Sin game da samar da al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama, da kuma manyan tsare-tsare guda uku na duniya, da tabbatar da yin ciniki cikin ‘yanci da tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da hada karfi da karfe wajen kare adalci a duniya. Wadannan yarjejeniyoyi za su haifar da karin kwanciyar hankali ga zaman lafiya da ci gaban duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp