A kalla ‘yan bindiga 12 ne jami’an tsaro suka kashe inda suka kwato dabbobin da aka sace tare da kwato makamai a karamar hukumar Kurfi-Safana ta jihar Katsina.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Nasiru Mua’zu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce an kaddamar da farmakin ne a matsayin martani ga harin da aka kai da sanyin safiyar yau Laraba a kauyen Rahamawa da ke gundumar Kuraye a karamar hukumar Charanchi.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 4 Da Manoma A Katsina
- Mutane Hudu Sun Mutu, An Ceto Wasu A Hatsarin Kwalekwale A Yauri
Mua’zu ya ce maharan sun afkawa al’ummar ne da misalin karfe 5:40 na safe, inda suka raunata wani Alhaji Danmalam mai shekaru 60, tare da yin awon gaba da shanu 22.
Da take aiwatar da rahotannin sirri cikin gaggawa, rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yansandan Nijeriya, Sojoji, jami’an kula da jama’a na jihar, da ’yan banga na yankin sun bi sawun barayin da suka tsere zuwa Dutsen Falale da ke yankin Kurfi-Safana inda aka yi musayar wuta mai tsanani, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindigar 12.
Sai dai kuma, yayin da yake yabawa wannan bajinta da jajircewa da jami’an tsaron suka yi, Dakta Mua’zu ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar wani dan banga mai suna Alhaji Danmalam wanda ya rasa ransa a fafatawar.
Bugu da kari, soja guda ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana samun kulawa a Asibiti.
Alhaji Danmalam ya rasu ne sakamakon harbin bindiga a cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko da ke Charanchi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp