Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana shirye-shiryen kwaso ‘yan Nijeriya da suka makale a kasashen Isra’ila da Iran. Wannan mataki na zuwa ne bayan barkewar sabon rikici tsakanin kasashen biyu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a daren Talata, an bayyana cewa ofisoshin jakadancin Nijeriya a Tel Abib (Isra’ila) da Tehran (Iran) na kokarin tuntubar ‘yan Nijeriya domin tabbatar da dawowar su cikin aminci.
- EFCC Ta Kama Tsohon Kakakin Majalisar Filato Da Wasu ‘Yan Majalisa 14 Bisa Zargin Almundahana
- APCn Kaduna Ta Mara Wa Tinubu, Uba Sani Da Kakakin Majalisa Abbas Baya Don Wa’adi Na Biyu
An shawarci duk ‘yan Nijeriya da ke wadannan kasashe da su kiyaye dokoki da matakan tsaro na cikin gida, tare da tuntubar ofishin jakadancin Nijeriya mafi kusa domin yin rijista da samun karin bayani.
Ma’aikatar ta yaba da jajircewar ma’aikatan jakadancin Nijeriya a kasashen biyu, tare da tabbatar da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin kare lafiyar ‘yan Nijeriya a kasashen waje.
Sanarwar ta kara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na kasa da kasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro.
Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin karshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a wadannan kasashe.
“Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntubar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun karin umarni.”
Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da fada tsakanin Isra’ila da Iran, tare da bukatar bangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare hakkin dan Adam na duniya, kuma su bai wa rayuwar fararen hula muhimmanci.
Ma’aikatar ta jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan hanyoyin warware rikici ta hanyar lumana da kuma tallafa wa zaman lafiya a yankuna da duniya baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp