Gwamna Ahmed Aliyu na jihar ya kaddamar da shirin musamman na saukakawa ma’aikata rage radadin tsadar farashin abinci a dalilin cire tallafin man fetur da gwamnati mai ci ta yi.
Shirin na musamman wanda Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya kaddamar a ranar Laraba mai taken “Shagon sauki na Ahmadun Alu”, gwamnatin Sakkwato ta bayyana cewar daya ne daga cikin shirye-shiryenta na inganta jin dadi da walwalar jama’a.
- Mutane 4 Sun Mutu, 10 Sun Jikkata Yayin Da Wata Mota Ta Taka Bam A Borno
- Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida
Gwamna Namadi da ya jagoranci bikin kaddamarwar ya yaba wa Aliyu kan kokarin da yake yi na sauke nauyin da ke kansa ta hanyar assasa ayyukan da za su yi tasiri ga al’umma.
Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas.
Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp