An watsa shirin talibijin mai taken “Yawon bude ido a Tuscany” a Florence na Italiya, da babban rukunin gidan radiyo da talibijin kasar Sin CMG da hukumar yawon bude ido ta yankin Tuscany na Italiya suka tsara da kuma gabatar cikin hadin gwiwa. Shugaban CMG Shen Haixiong da babban jami’in hukumar sun shaida bikin gabatarwar, kuma sun yi musanyar ra’ayi mai zurfi game da daukar shirye-shirye cikin hadin gwiwa da gabatar da albarkatun yawon bude ido da kiyaye al’adu da sauransu. (Amina Xu)