A ranar Litinin ne kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kudi ya gayyaci Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin Wutar lantarki ta Nijeriya (TCN), Sule Abdulaziz, kan cinikin kayan aikin wutar lantarki ta Azura da ya kai dala Miliyan 33 na kamfanin Neja Delta Power Holding Company.
Mai bada umarni kan rarraba wutar lantarki, Victor Adewumi da sauran masu fada aji na kamfanin TCN a ranar Litinin din da ta gabata duk sun hallara a gaban kwamitin da ke binciken shirin sayar da kamfanin samar da wutar lantarki na kasa (NIPP) da ofishin sayayya na gwamnati ke yi.
Adewumii ya ce, tashar wutar lantarki ta Azura da ke jihar Edo ya kamata ta samar da megawatt 450, amma bisa wasu dalilai wutar bata kaiwa. Takardar da aka gabatar wa kwamitin ta nuna cewa, Azura ta samar da megawatt 1,755.9 ne kacal a cikin wani dan lokaci.
Shugaban kwamitin, James Faleke, ya ce iyakan abinda tashar wutar lantarki ta Azura ke yi ya saba wa yarjejeniyar da aka rattabawa hannu.
Ya ce: “’Yan Najeriya a shirye suke su kafa masana’antu, amma babu dama. Duk da haka kuma suna biyan makudan kudade wajen biyan kudin wutar. Wannan zamba ba batu ne kawai da ya shafi kamfanin TCN ba, ya shafi Nijeriya baki daya”