Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Laraba a taron manema labaru da aka gudanar cewa, kayayyakin Sin sun shiga kasuwar duniya, inda suka kara baiwa masu sayayya na kasa da kasa damar samun zabi. Jami’ar ta yi tsokacin ne bisa yadda batun wasu kayan shayi na kasar Sin ya jawo hankalin sassan kasa da kasa, bayan shigarsu kasuwar hannun jari ta kasashen waje.
Mao Ning ta bayyana cewa, kayayyakin Sin sun kara jawo hankulan masu sayayya na kasa da kasa ta hanyar fasahohi, da shaida al’adun gargajiya, da zane-zane da suke dauke da su, da kuma abubuwan dake hade Sin da kasashen waje. Daga kayayyaki kirar kasar Sin zuwa tambarin kayayyakin Sin, kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci, bisa tsarin masana’antunta mai inganci, da kasuwa mai adalci da bude kofa, da kuma kokarin yin kirkire-kirkire a dogon lokaci.
Hakazalika kuma, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin tana maraba da kayayyakin kasashen waje masu inganci, da su shiga kasuwarta, su more fasahohi da samun ci gaba tare, ta yadda al’ummun kasa da kasa za su amfana daga hanyoyin raya tattalin arzikin duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp