Ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta kira taron karawa juna sani na kamfanonin kere-kere karo na 15, inda aka mai da hankali kan aikin raya sana’o’i masu inganci da suka shafi samar da wutar lantarki daga zafin rana.
A yayin taron, an yi kiran warware matsalar takarar farashi da bai kamata ba bisa dokokin kasa, tare da karfafa ingancin kayayyakin samar da wutar lantarki daga zafin rana, yayin da ake kawar da tsoffin kayayyaki cikin tsari, domin cimma burin neman dauwamammen ci gaban sana’o’in.
Cikin ’yan shekarun nan, sana’o’in samar da wutar lantarki daga zafin rana sun bunkasa cikin sauri a kasar Sin. A halin yanzu, kasar tana kan gaba cikin kasashen duniya a fannonin bunkasuwar sana’o’in, da fasahar da abin ya shafa, da yawan kasuwannin dake amfani da fasahar da dai sauransu. A nan gaba kuma, kamfanonin da abin ya shafa za su dukufa kan aikin nazarin sabbin fasahohi, da tabbatar da tsaron aikin, yayin da suke karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kamfanonin kasashen duniya, domin kara karfi da ingancin kayayyakin samar da wutar lantarki daga zafin rana da kasar Sin take kerawa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp