Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Mahamoud Ali Yousouf ya yabawa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar AU cewa, kasar Sin a matsayin aminiya ce da za a iya dogaro da amincewa da ita.
A yayin da yake karbar takardar wakilcin kasa daga sabon shugaban tawagar jakadun kasar Sin dake kungiyar AU Jiang Feng, Mahmoud Yousouf ya bayyana cewa, kungiyar AU tana son karfafa mu’amala da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, domin samar da tabbaci ga kasashen duniya dake fama da sauye-sauye a halin yanzu.
A nasa bangare kuma, Jiang Feng ya mika gaisuwa da fatan alheri na shugabannin kasar Sin ga shugaba Yousouf, ya kuma yaba wa kungiyar AU bisa babbar gudummawar da ta bayar ga aikin shimfida zaman lafiya da zaman karko a nahiyar Afirka, da jagorantar dunkulewar kasashen Afirka, da kuma yin kira da a nuna adalci ga kasashen Afirka da sauransu. Haka kuma, ya ce kasar Sin tana son hada kai da kungiyar AU wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing, tare da gina makomar al’ummomin Sin da Afirka ta bai daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp