Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a jiya Juma’a, inda suka alkawarta hada gwiwa wajen ingiza cudanyar mabanbantan sassa, da karfafa hadaka wajen yaki da tashe-tashen hankula da danniya ke haifarwa, da fito-na-fito tsakanin bangarori daban daban.
Shugaba Macron, ya ce Faransa da Sin sun amince da wasu muhimman batutuwa masu yawa, ciki har da goyon bayan cudanyar mabanbantan sassa, da martaba dokokin kasa da kasa. Kazalika, bangaren Faransa na fatan karfafa tsare-tsaren manufofi tare da Sin, a fannin raya tattalin arzikin duniya, da tsarin jagorancin hada-hadar kudade na duniya, kana za su yi aiki tare wajen shawo kan tarin kalubalen dake addabar duniya, da sanya sabon kuzari ga cudanyar mabanbantan sassa, da dakile yiwuwar fadawar duniya cikin tashe-tashen hankula da danniya ke haifarwa, da fito-na-fito tsakanin bangarori daban daban.
A nasa bangare kuwa, Wang Yi ya ce Sin da Faransa kawaye ne dake da cikakkiyar dangantaka bisa manyan tsare-tsare, kana sun kasance manyan kasashe biyu masu tasirin samar da daidaito ga duniya. Har ila yau, Sin a shirye take ta karfafa tattaunawa, da hadin gwiwa tare da Faransa, da hada kai don wanzar da salon cudanyar mabanbantan sassa, da adawa da tsarin danniya daga bangare guda, da nuna kin jinin fito-na-fito daga wani bangare, ta yadda za a kai ga shigar da karin tabbaci, da damar yin kyakkyawan hasashe ga duniya mai fuskantar sauyi da hargitsi, da ingiza tasirin daidaito, da oda ga jagorancin mabanbantan sassan, da raya tattalin arzikin duniya mai gamewa, da haifar da gajiya ga kowa, kana da aiki tare wajen gida al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp