A ranar Asabar, ƙungiyar PSG ta doke Bayer Munich da ci 2-0 a wasan zagayen kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya na Kungiyoyi, wanda aka buga a filin wasa na Mercedes Benz, Atlanta, Amurka. Duk da samun katin kora guda biyu, PSG ta nuna kwarewa da jajircewa wajen zura ƙwallaye masu kyau a raga.
A wani wasa da aka buga a daren ranar Asabar a filin wasa na MetLife Stadium, New Jersey, Real Madrid ta doke Borussia Dortmund da ci 3-2. Madrid ta fara da ƙwallaye biyu daga Gonzalo Garcia da Fran Garcia, kafin Dortmund ta yi ƙoƙarin dawo da wasan. Kylian Mbappé ya ƙara wa Madrid ƙwallo ta uku da kyakkyawan bugun watsiya, sai dai Dortmund ta rama da bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan Dean Huijsen ya samu jan kati.
Yanzu Real Madrid za ta fuskanci PSG a zagayen wasan kusa da na ƙarshe, wasan zai gudana ranar Laraba, 9 ga Yuli, a MetLife Stadium da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Wanda ya ci zai ci gaba zuwa wasan ƙarshe inda zai hadu da wanda ya yi nasara tsakanin Fluminense da Chelsea.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp