Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana a jiya Asabar cewa, kasar Sin a shirye take wajen yin aiki da Brazil domin samun moriyar juna, da fadada hadin gwiwa a fannonin da suka shafi tattalin arzikin fasahar zamani, da na ci gaba mara gurbata muhalli, da kuma sabbin fasahohin kimiyya da na sha’anin jiragen sama.
Li ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva. A jiya Asabar ne firaministan kasar Sin ya isa birnin Rio de Janeiro domin halartar taron kasashen BRICS karo na 17.
- Arsenal Ta Kammala Daukar Martin Zubimendi Daga Real Sociedad
- Bayern Munich Ta Fara Zawarcin Marcus Rashford
Da yake bayyana kasashen biyu a matsayin masu goyon bayan tsarin damawa da bangarori daban-daban da cinikayya cikin ‘yanci, Li ya ce, kasar Sin tana da muradin inganta sadarwa da yin hadin gwiwa da Brazil bisa tsare-tsaren da suka kunshi damawa da sassa daban-daban kamar MDD, da kawancen BRICS da kungiyar G20, da yin aiki tare da kasashe masu tasowa wajen sa kaimi ga karfafa samun duniya mai daidaito da kyakkyawan tsari, da samar da moriyar kasa da kasa ta bai-daya, da dunkulewar tattalin arzikin duniya, da samar da karin tabbaci da kuma kwanciyar hankali ga duniya baki daya.
A nasa bangaren, Lula ya bayyana cewa, Brazil a shirye take ta inganta mu’amala da hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da kimiyya da fasaha, da sha’anin kudi, da bangaren jiragen sama.
Kazalika, ya kara da cewa, Brazil tana son zurfafa sadarwa na bangarori daban-daban da gudanar da tsare-tsare a tsakaninta da kasar Sin, tare da hada karfi da karfe wajen nuna adawa da babakeren bangare guda, da kiyaye tsarin damawa da bangarori masu yawa, da cinikayya cikin ‘yanci, ta yadda za a karfafa zaman lafiya da ci gaban duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp