Sanata Henry Seriake Dickson, Shugaban kungiyar ‘Yan Majalisar Dattawa daga yankin Kudu- Maso Kudu ya bayyana cewar wajibi ne yankin ya haɗa kai ya dauki matsaya guda kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa.
A bayanin da mataimakinsa kan yaɗa labarai a Arewa Jamilu Abubakar ya fitar, Sanatan ya jagoranci zaman jin ra’ayoyi ne kan korafe- korafe game da bukatun kafa jihohi da kananan hukumomi, batutuwan da suka shafi jinsi, gyaran tsarin zabe da sauransu a Ikot Ekpene da ke jihar Akwa- Ibom.
- Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
- Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha
Ya ce bambancin kabilu da al’adu da harsuna a yankin Kudu-maso Kudu ba za su zama cikas ba, sai dai a yi amfani da su wajen ci gaban al’ummar yankin baki daya.
Dickson wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a taron sauraren ra’ayin al’ummar yankin wanda ya jagoranta.
Sanatan ya bayyana cewar shugabannin yankin na baya sun gina yankin a kan al’adar hadin kai domin shawo kan bambancin al’adu da harsuna tun kafin samun ‘yancin kai.
Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu.
A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp