Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kan ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi a jihar.
A wata ziyara ta jaje da ya kai wa gwamnan Kano kan rasuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata, Sambo ya nuna gamsuwa kan irin ci gaban da ake samu a fannin gine-gine da kyautata gine-ginen gwamnati, musamman gyaran gidan gwamnatin Kano.
- Abba Ya Yi Sabbin Naɗe-naɗe A Jihar Kano
- Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
Namadi, Ya bayyana cewa yana bibiyar ayyukan gwamnatin Abba Yusuf. Ya kuma ya shaida irin sauye-sauyen da aka samu a zahiri.
Gwamna Yusuf ya gode wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar, bisa ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar tare da kalaman karfafa guiwa, yana mai jaddada ƙudirin gwamnatinsa na farfaɗo da martabar Kano ta hanyar ayyukan raya kasa.
A wani labarin makamancin wannan, Sanata Abubakar Sani Bello da wasu manyan baki sun kai ziyarar jaje ga gwamnan da al’ummar Kano dangane da rasuwar Alhaji Dantata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp