Hukumar raya kasa da aiwatar da gyare gyare ta kasar Sin (NDRC) ta ce kasar za ta kara daukaka tsarin wuraren cajin lantarki da gina tsarin ta yadda zai zama mai inganci da ingantaccen lantarki da kyakkyawan fasali, da amfani da fasahohin zamani.
NDRC da wasu hukumomin gwamnati 3 sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa game da bangaren a yau, inda suka ce wuraren cajin ababen hawa masu amfani da lantarki na da muhimmanci matuka wajen goyon bayan raya masana’antar kera ababen hawa masu amfani da lantarki da ginin sabon tsarin samar da lantarki tare da rage fitar da hayakin Carbon a bangarorin sufuri da na makamashi
Zuwa karshen shekarar 2027, kasar Sin na sa ran samun sama da wuraren caji 100,000 a fadin kasar, tare da daukaka ingancin hidimomi da amfani da fasahohi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp