An rufe taron shugabannin BRICS karo na 17 a Rio de Janeiro hedkwatar Brazil a ran 7 ga watan nan da muke ciki agogon kasar. Taron ya fitar da sanarwar Rio de Janeiro, inda aka kai ga matsaya daya kan batun raya fasahar AI da tinkarar sauyin yanayi da dai sauran bangarori.
An yi wannan taro ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar dimbin sauye-sauye. Mabambantan bangarori na ganin akwai matukar bukatar yi wa tsarin daidaita harkokin duniya kwaskwarima cikin gaggawa. To, wace rawa kasar Sin za ta taka game da wannan batun, duba da matsayinta na babban ginshiki a BRICS?
- Akwai Bukatar Sin Da Masar Su Zurfafa Hadin Gwiwa Domin Kare Muradunsu
- Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa
Bari mu yi bayani. Kwanan baya, Sin da sauran mambobin BRICS sun yi iyakacin kokarin tabbatar da shimfida zaman lafiya a duniya. Wannan karo kuwa, Sin ta nanata wajibcin kasashe mambobin BRICS su jagoranci tabbatar da adalci, kana su yi kokarin tabbatar da da’a da adalci, sannan su karfafa magance rigingimu ta hanyar zaman lafiya, da warware matsaloli bisa gaskiya da hakkin abubuwan da ke faruwa.
Game da koma bayan tattalin arziki da duniya ke fuskanta, ana matukar bukatar bullo da sabbin hanyoyin samun bunkasa. Shi ya sa, yin kirkire-kirkire da habaka hanyoyin samun bunkasa, ya zama mataki mafi jawo hankula daga cikin tsarin hadin gwiwar mambobin BRICS. Sin ta sanar a wannan taro cewa, za ta kafa cibiyar nazarin sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ta Sin da kasashen mambobin BRICS.
Kazalika, game da babakeren da Amurka ke nunawa, mambobin BRICS sun yi kira da a kiyaye ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori a duniya da gaggauta kafa kyakkyawan tsari da dokar tattalin arziki da cinikin duniya mai adalci da bude kofa. Albarkacin cika shekaru 10 da kafuwar bankin NDB na BRICS, Sin na goyon bayan bankin da ya kara karfinsa don daga matsayin hadin gwiwar kasa da kasa a bangaren harkar hada-hadar kudaden duniya.
Dadin dadawa, a shekaru 20 da suka gabata, tsarin hadin kan BRICS na zama muhimminyar alamar dunkulewa da hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka fi dacewa nan gaba, don gaggauta bunkasar wannan nagartaccen tsari da bai wa duk fadin duniya tabbaci, wadda ke fuskantar dimbin matsaloli da dimbin kalubale da sauye-sauye. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp