Kocin Paris Saint-Germain (PSG), Luis Enrique, ya bayyana cewa wasan da ƙungiyarsa za ta fafata da Real Madrid a daf da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin Duniya zai kasance “na musamman“. Sai dai Enrique ya kaucewa magana kan tsohon ɗan wasansa, Kylian Mbappé, wanda yanzu ke buga wasa a Real Madrid.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a filin wasa na MetLife da ke kusa da birnin New York, Enrique ya ce duk lokacin da aka yi wasa da Real Madrid, wannan wasa ba ƙaramin abu ba ne. Yayin da PSG ke kokarin cigaba da jan zarenta bayan nasararta a kakar bana, Xabi Alonso na Real Madrid shima na fatan lashe kofinsa na farko a matsayin koci.
- Modric Zai Bar Real Madrid Bayan Kammala Gasar Cin Kofin Duniya Na Kungiyoyi
- NIS Ta Yi Wa Manyan Jami’ai 98 Ado Da Sabbin Muƙamansu
PSG ta zo gasar da kwarin gwuiwa bayan ta lashe gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League a karo na farko a tarihinta. Wasan da za su buga da Real Madrid na zuwa ne bayan tafiyar Mbappé zuwa Madrid, inda Enrique ya horar da shi a kakarsa ta ƙarshe a PSG. Mbappé ya sha fama da ƙin saka hannu kan sabon kwantiragi, wanda ya sa aka dinga dakatar da shi daga buga wasanni a wancan lokaci.
Enrique ya ce, “Wannan wasa na da matuƙar muhimmanci, ba wai kawai saboda suna Real Madrid ba, amma kuma saboda muna kusa da wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya.” Ya ce nasara a wannan wasan zai buɗe musu ƙofar zuwa wasan ƙarshe da zai kasance babban abin alfahari ga ƙungiyar.
Duk wanda ya samu nasara a wasan PSG da Real Madrid zai haɗu da Chelsea a wasan ƙarshe a ranar Lahadi. Chelsea ta samu nasarar doke Fluminense da ci 2-0 a zagaye na huɗu, wanda ya sa ta samu gurbin wasan ƙarshe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp