Shugaban Kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Kasa (NUMHP), Dakta Kabiru Mohammad Nabargu ya bayar da tabbacin cewa Hukumar Kulla da Inganci Abinci ta Kasa ( NAFDAC) tare da kungiyarsu sun kudiri aniyar tsabtace sana’ar bayar da magungunan gargajiya a fadin kasar nan baki daya.
Dakta Kabiru ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan kammala wani taron da kungiyar ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar NAFDAC, wanda aka gudanar da shi a dakin taro na gidan Sardauna da ke Jihar Kaduna.
Ya ce ganin yadda mutane da dama da ba su san harkar maganin gargajiya ba suke shiga sana’ar wanda ke kawo cikas, inda ya ce ya zama wajibi su dauki matakin tsabtace sana’ar don kare mutuncin sana’ar tare da nuna musu muhimmacin yin rajista da hukumar NAFDAC domin tabbatar da ingancin maganin da suke sayarwa.
“Yanzu lamarin ya kai matakin da mutum zai debo itatuwa a daji ya shiga daki ya yi maganin da ba shi da rajista kuma yana sayar wa al’umma, wanda hakan ya saba wa dokar sayar da magani, saboda haka ya sa muka gayyato shugaban hukumar NAFDAC na shiyyar Arewa maso yamma da ya zo ya yi mana bayani irin tanadin da suka yi da kuma wayar da kan masu maganain gargajiya kan muhimmacin yin rajista kamin su fitar da shi kasuwa,” in ji shi.
Shugaban ya ce galibin masu fakewa da sana’ar magungunan gargajiya suna cutar mutane ba su da rajista da kungiyarsu da hukumar lafiya ko NAFDAC. Ya ce a kokarinsu na tsabtace harkar magungunan gargajiya da kare martabar sana’ar ya sanya suka hada hannu da hukumar NAFDAC domin taimaka wa duk wani mai sana’ar maganin gargajiya yin rajista domin samun natsuwa wajen gudanar da sana’arsu a fadin kasar nan baki daya.
A nasa jawabin, shugaban hukumar NAFDAC na shiyyar Arewa maso yamma, Nantim Dadi Mullah, ya bayyana gamsuwarsa dagane da matakin da kungiyar masu maganain gargajiya ta kasa ta dauka na kawo tsabta a sana’arsu.
Ya tabbatar da cewa NAFDAC ta amince za ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar domin ganin duk wani mai sana’ar maganin gargajiya ya yi rajista da hukumarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp