Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, ya jinjinawa gudunmuwar kasar Sin ga ci gaban kasarsa.
Da yake jawabi jiya a fadar shugaban kasar yayin da yake bitar ziyara ta baya-bayan nan da ya kai Amurka, shugaba Embalo ya ce kasar Sin abokiyar hulda ce ta hakika, kuma sahihi yayin da take bayar da taimako.
Ya ce babu wanda ke gindaya sharudi a hadin gwiwarsu da Sin, yana mai nanata cewa Guinea Bissau kasa ce mai cikakken ‘yanci kuma ‘yar ba ruwanmu.
A cewarsa, kasar Sin ta kasance abokiyar kasar tun farko kuma ba ta taba watsi da su ba. Yana mai bayyana ta da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin mai matukar inganci. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp