Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya nuna ƙaduwarsa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana mai cewa Nijeriya ta rasa ɗaya daga cikin manyan shugabanninta.
A cikin saƙon ta’aziyya, Shettima ya ce Buhari ya yi rayuwar gaskiya da sadaukarwa wajen haɗa kan ‘yan ƙasa.
- Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
- Na Shiga Aikin Soja Domin Gujewa Yin Auren Fari Da Ƙuruciya — Buhari
Shettima Ya roƙi Allah ya jikansa da gafara, ya kuma ba iyalansa da ’yan Nijeriya haƙuri da juriyar rashinsa.
Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da yin addu’o’i ga marigayin da kuma yin koyi da kyawawan dabi’unsa domin ci gaban ƙasa.
Shettima dai ya isa birnin Landan domin rako gawar marigayi, Muhammadu Buhari zuwa gida Nijeriya, inda ake sa ran yi masa sutura a mahaifarsa ta Daura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp