Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya bayyana cewa, za a gudanar da taron shugabannin matasa na farko na dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro na kasar Sin da Afirka a birnin Nanjing, daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Yulin nan, inda kusan manya da matsakaitan hafsoshin soja kusan 90 daga kasashen Afirka fiye da 40 za su halarta.
Jiang ya kara da cewa, an shirya taron ne da nufin aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika da aka yi a birnin Beijing, da kara cimma matsaya, da karfafa hadin kai da fadada hadin gwiwa a fannin zaman lafiya da tsaro, da ba da gudummawa ga gina al’ummar da ta dace da dukkan fannoni mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga Sin da Afirka a sabon zamani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp