Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majaliar gudanarwar kasar Sin ya yi wani taron manema labarai, inda mataimakin darektan hukumar kwastan ta Sin Wang Lingjun, ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, Sin da Amurka na kokarin tabbatar da ci gaban da aka samu na yarjejeniyar London.
Sin ta sake nanata matsayin da take daukawa cewa, ba cikin sauki ba ne aka cimma matsaya daya a Geneva da yarjejeniyar London ba, kuma ba za a samu mafita ta hanyar matsa lamba da yin yaudara ba, sai idan an yi shawarwari da hadin gwiwa. Sin na fatan Amurka ta bi hanya iri daya tare da ita, don ganin Sin da Amurka sun koma hanyar hadin gwiwa a bangaren ciniki da tattalin arziki, ta yadda za a gaggauta ganin tsarin ciniki na duniya ya koma hanyar adalci da bude kofa, matakin da zai taka rawar gani ga farfadowa da bunakasar tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp