Kwanan baya, mahaukaciyar guguwa mai lakabin “Danas” ta ritsa kudancin yankin Taiwan na kasar Sin, tare da haifar da munanan asarori ga al’ummar wurin, inda wasu wurare suka yi fama da katsewar wutar lantarki na tsawon fiye da kwananki 7 a jere. Abu mafi bakin ciki shi ne, saboda kasa samun wutar lantarki, wata tsohuwa ta rasa ranta sakamakon gobara da kyandir ta haddasa. Duk da matsalolin da ake fuskanta wajen gudanar da aikin ceto, jagoran yankin na Taiwan Lai Ching-Te ya nuna halin ko-in-kula ga aikin ceto, har ma bai je wurin da bala’in ya shafa kan lokaci ba, ya kuma umurci al’ummar da ke fama da bala’in da su dogara da kansu wajen ceton kansu, har ma ya yi kalaman cewa wai “sojoji ba za su iya shiga gidajen jama’a don ba da taimako ba”, don guje wa daukar alhakin taimaka wa jama’a. Matakin da ya janyo suka matuka daga wajen al’ummar yankin.
Amma me ya sa hakan? Watakila duk karfinsa ya kare ne wajen gabatar da jawabai masu taken wai “Laccoci guda 10 game da hadin kan al’umma”, wadanda ke yunkurin tallafawa ra’ayin “ballewar yankin Taiwan daga jamhuriyar jama’ar kasar Sin”.
A lokacin da “Hadin kai” ya zama wuka ko takobin kawar da masu bambancin ra’ayi, kuma “Kirki” ya zama abin da ke rura wutar kiyayya, to wa zai bi irin wannan “Jagora”? Sam Lai Ching-Te bai cancanci zama jagoran yankin Taiwan ba. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp