A kwanan baya ne aka kaddamar da taron shugabannin matasa na dandalin zaman lafiya da tsaro na kasar Sin da kasashen Afirka a birnin Nanjing, fadar mulkin lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, inda manya da matsakaitan hafsoshin soji 80 na kasar Sin da na kasashen Afirka fiye da 40 suka halarta.
An gudanar da taron ne bisa taken “fuskantar makoma da gina zaman lafiya tare”. Mahalarta taron na kasashen Sin da Afirka sun tattauna batutuwan da suka shafi “Inganta kwazon aiki domin samar da zaman lafiya da tsaro a Afirka”, da “Hanyoyin samar da fasahohin da za su karfafa hadin gwiwar tsaro”, da “Cikakken tsarin magance barazanar tsaron da ba a saba gani ba”, inda suka amince da nasarorin da aka samu a hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin zaman lafiya da tsaro. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp