Yayin bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya wato CISCE karo na uku, mataimakin shugaban kamfanin Panasonic Homma Tetsuro, ya bayyana wa ‘yan jarida na babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG cewa, yawan kamfanonin kasar Sin da suke samar da sassan kayayyaki ga kamfaninsa ya kai dubu 6, wanda ya kai kashi 1 cikin 3 na adadinsu a duk duniya. Ga kamfanin Panasonic, kasar Sin kasa ce mafi girma ta kera kayayyaki da yin nazari da kuma saye-saye, don ya ce, yana son amfani da damar bikin CISCE wajen kara gano kamfanonin samar da kayayyaki na kasar Sin.
Homma Tetsuro ya yi nuni da cewa, yana fatan kayayyakin da aka samar za su dace da yanayin kasar da aka sayar da su, kuma ya kamata tsarin samar da kayayyaki ya dace da yanayin kasar da aka sayar da su a fannonin yin nazari, da yin sayayya, da samar da su, da kuma zanen kayayyakin, kuma wannan ne burin tawagar kamfanin Panasonic da za ta kasance a kasar Sin na dogon lokaci a halin yanzu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp