Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron ƙarar zargin almundahana ta naira biliyan ɗaya da ake yi wa Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Lawan Malumfashi, da wasu jami’ai biyu har zuwa 24 ga Nuwamba, 2025.
Kwamishinan KANSIEC mai kula da Harkokin Shari’a, Barr. Muntari Garba Dandago, ya bayyana cewa Mai Shari’a J.J. Malik ya ɗage shari’ar ne domin a tabbatar da isar da takardun kotu ga dukkan masu laifi, da kuma tabbatar da halartar su a kotu domin fara shari’a.
- Kotu Ta Kori Shugaban KANSIEC Da Wasu Mutane 5 A Kano
- KANSIEC Ta Sanya 10m A Matsayin Kuɗin Fom Na Takarar Ciyaman A Kano
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ce ta shigar da ƙarar Farfesa Malumfashi da Sakataren Hukumar, Anas Muhammed Mustapha da kuma Daraktan Kuɗi na Hukumar, Ado Garba.
Ana zargin su da hada baki a tsakanin watan Nuwamba da Disamba 2024, wajen wanke kuɗaɗen gwamnati ta hanyar mu’amala da kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar ƙarar, KANSIEC ƙarƙashin jagorancin Farfesa Malumfashi ta canja wurin ₦1.02 biliyan daga asusun bankin Unity zuwa kamfanin SLM Agro Global Farm, wanda ba shi da wata yarjejeniya da hukumar.
Masu ƙarar sun bayyana cewa an ce an bai wa kamfanin kuɗin ne domin samo kuɗin hannu don biyan ma’aikatan wucin gadi da aka ɗauka a zaɓukan ƙananan hukumomi na 2024. Daga bisani kuma, an ce an dawo da kuɗin a matsayin tsaba zuwa hukumar.
Lauyan ICPC, Barr. Enosa Omoghibo, ya shaida wa kotu cewa an shirya fara gurfanar da waɗanda ake zargi ne, amma “ba su halarci kotu ba.”
Sai dai Lauyan waɗanda ake ƙarar, M.A. Magaji (SAN), ya ce abokan hulɗarsa ba su samu takardun shigar da ƙara kotu ba. Ya ƙara da cewa isar da takardu abu ne mai muhimmanci kafin kotu ta iya ci gaba da shari’a.
Daga nan ne kotu ta dage ci gaba da shari’ar zuwa 24 ga Nuwamba, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp