Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya, Super Falcons, ta samu nasarar kaiwa wasan ƙarshe na gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025 da ake bugawa a ƙasar Moroko, bayan ta doke Afirka Ta Kudu da ci 2-1 a filin wasa na Larbi de Zouli da ke birnin Casablanca a yau Talata.
An buga wasan da misalin ƙarfe 5 na yamma agogon Nijeriya, kuma dimbin magoya bayan Super Falcons sun shaida wasan a filin wasa da kuma gidajen kallon kwallo a faɗin ƙasar domin nuna goyon baya ga tawagar matan ƙasa.
- An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka
- Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu
- Mataimakin Shugaban Kamfanin Panasonic: Kamfanonin Sin Dake Samar Da Sassan Kayayyaki Ga Kamfaninsa Sun Kai Dubu 6
Kyaftin ɗin tawagar, Rasheedat Ajibade, ce ta fara zura kwallo a ragar Afirka Ta Kudu, bayan ta samu dama a bugun daga kai sai mai tsaron gida kafin hutun rabin lokaci. Bayan komawa daga hutun, Afirka Ta Kudu ta farke ta hannun Maserame Mothlhalo a minti na 60 da fara wasa.
Yar wasan gaba ta Nijeriya, Chinwendu Alozie, ce ta tabbatar da nasara da kwallon da ta jefa kafin tashi daga wasan. Wannan nasara ta ba wa tawagar ta Justin Madugu damar kaiwa wasan ƙarshe na gasar.
Yanzu haka, Super Falcons za su kara da ƙasar da za ta yi nasara tsakanin Moroko, wacce ke masaukin baki, da Ghana, a wasan da za a buga daga baya a yau Talata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp