Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a taron manema labaru da aka saba shiryawa Larabar nan cewa, a yayin da ake fama da koma baya a fannin samar da kayayyaki a duniya, da ma raunin ci gaban tattalin arzikin duniya, layin dogon dakon kaya tsakanin Sin da Turai ya bude sufurin jiragen kasa dubu 10 gabanin lokacin da aka tsara, lamarin dake zama wani labari mai karfafa gwiwa.
Rahotanni sun nuna cewa, jirgin kasa na dubu 10 tsakanin Sin da Turai a bana, ya isa nahiyar Turai kwanaki 10 kafin lokacin da aka tsara kan na shekarar bara.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp