Fitaccen lauya kuma mai rajin kare ‘yancin ‘yan Adam, Femi Falana ya yi zargin cewa, hukumar tsaron farin kaya ta DSS, a asirce ta ayyana yunkurin kamo gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele.Â
Falana, a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, ya ce, DSS ta ayyana cafko Godwin ne bisa zargin ta’addanci, inda lauyan ya koka da cewa, wannan abin da DSS ta yi abu ne mai daure kai matuka.
A cewarsa, ba tare da wata fargaba ba, zan iya cewa, a lokacin da DSS ta ayyana cafko Godwin, bai cikin kasar nan, amma hukumar a asirce ta ayyana son cafko shi, inda ya yi nuni da cewa, irin wannan na faruwa ne kawai a jamhuriyar da babu ita.
Ana dai zargin Godwin ne da badakalar daukar nauyin aikata ta’addanci da karkatar da haraji da kudaden bayar da rancen aikin noma da kuma harkallar kudaden musaya na waje, wanda kuma hakan ya sa Godwin ya gaza bayyana a gaban majalisar kasa don amsa tambayoyi akan sake sabbin kudi da kuma adadin kudin da za iya fitarwa bankunan fadin Nijeriya.