A cikin mako na biyu, an samu koma baya a kasuwar sayar da hannun jari, inda masu zuba hannun jari a kasuwar suka yi asarar da ta kai Naira biliyan 365.
A makon da ya gabata kasuwar ta samu raguwar zuba hannun jari da ta kai ta Naira tiriliyan 66.352 daga Naira tiriliyan 66.717 da aka samu a makon da ya gabata.
- ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
- Dantsoho Ya Nemi Masu Zuba Hannun Jari Da Su Ci Gajiyar Tsarin EPT Na NPA
Ɗaukacin shiyar da aka sayar da kasuwar, a makon da ya gabata, ta kai kaso 0.55, inda ta kulle a kan a 105. 955.13 daga 106,538.60, ana wanda aka samu a makon da ya gabata.
Kazalika, a makon da ya gabata a ranar Lintinin kasuwar ta dan farfado, inda masu zuba hannun jari suka samu raibar Naira biliyan 52.17, sai dai, kasuwar ta rufe da yin asara a ranar Talata inda masu zuba hannun jari a kasuwar suka yi asarar Naira biliyan 284.40.
Hakazalika, a ranar Laraba, masu zuba hannun jarin a kasuwar sun yi asarar Naira biliyan 48.45, inda kuma suka samu ribar Naira biliyan 81.76, a ranar Alhamis.
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43.
Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da masu zuba hannun suka yi.
Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818Â sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222.
Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune, kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da Bankin Jaiz Plc, sun sayar da shiyar da ta kai ta Naira biliyan 1.621, tare da karin Naira biliyan 3.244 da kuma wata hada-hadar Naira biliyan 1,528.
Hakan ya nuna cewa, an samu karin da ya kai na kaso 49.42 da kuma karin wani kaso 5.11 wanda ya nuna irin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta baki daya a kasuwar a cikin makon.
Kazalika, kamfanin sarrafa abincin dabbobi na Livestock Feeds Plc, ya samu karin farashin shiya mai yawa, inda ya samu kaso 22.16 sai kuma kamfanin Caverton Offshore Support Grp da ya samu farashin shiyar da ta kai karin kaso 15.38.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp