A karon farko a tarihi, adadin lantarki da kasar Sin ke iya samarwa ta karfin iska, da hasken rana ya zarce wanda ake iya samarwa ta amfani da dumi, inda alkaluman baya bayan nan suka nuna cewa ya zuwa karshen watan Maris da ya gabata, adadin lantarkin da kasar ta iya samarwa daga karfin iska da hasken rana ya kai kilowat biliyan 1.482, sama da adadin da kasar ta iya samarwa ta amfani da dumi.
Alkaluman da hukuma mai lura da harkokin makamashi ta kasar Sin ta fitar a yau Jumma’a, sun nuna yadda ake ta gaggauta fadada kayayyakin aiki masu nasaba da fannin, wanda hakan ke nuna yadda sashen makamashin lantarki daga karfin iska da hasken rana zai ci gaba da zama a sahun gaba sama da na dumi.
- Rage Farashin Man Fetur Na Dangote Ya Sa Wasu Gidajen Mai Na Kullewa
- Tuƙin Ganganci: Direba Ya Kashe Jami’in KAROTA
A cewar hukumar, cikin rubu’in farko na shekarar bana, adadin lantarkin da Sin ta samar daga karfin iska, da hasken rana ya kai kilowat biliyan 536.4 duk sa’a, wanda ya kai kaso 22.5 bisa dari na jimillar lantarkin da aka yi amfani da shi a kasar, kuma ya karu da kaso 4.3 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
Sashen masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, a gabar da ake ta aiwatar da managartan matakai na bunkasa tattalin arziki ba tare da fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi ba.
Tun daga shekarar 2013, adadin kayayyakin samar da lantarki daga karfin iska da aka kafa a Sin sun ninka har sau 6, yayin da na samar da lantarki daga karfin rana suka ninka sama da sau 180. Ya zuwa yanzu, sabbin kayayyakin samar da lantarki ta wannan hanya da ake kafawa duk shekara a kasar Sin, sun kai kaso sama da 40 bisa dari kan na daukacin kasashen duniya, adadin da ya yi matukar ba da gudummawa ga bunkasa duniya ta hanyar kaucewa gurbata yanayi. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp