A jiya ne, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin karo 40 dake gudana a Langfang da dandalin raya harkokin cinikayya ta yanar gizo na kasa da kasa tsakanin kasashe, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta gabatar da halin da ake ciki game da shigi da ficin da cinikayyar kayayyaki ta intanet tsakanin Sin da sauran kasashe a shekarar 2022, inda ta bayyana cewa, yanayin cinikayyar kayayyaki ta yanar gizo tsakanin kasashe, ya zarce Yuan tiriliyan 2 a karon farko, wanda ya kai Yuan tiriliyan 2.1, karuwar kashi 7.1 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2021. Kasuwancin intanet tsakanin kasashe, ya kara sanya wani sabon kuzari na ci gaban cinikayyar waje na kasar Sin.
Mai magana da yawun babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, kana daraktan sashen kididdiga da nazari Lyu Daliang, ya gabatar da cewa, a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, cinikayyar intanet tsakanin Sin da sauran kasashe ta samu bunkasuwa cikin sauri, kuma masu sayayya na duk fadin duniya suna samun karin zabi da sauki da kasuwancin intanet tsakanin kasashe ya samar.
Daga cikin wuraren da kasar Sin ke fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ta kafar intanet, kasuwar Amurka tana da kashi 34.3 cikin 100, yayin da Birtaniya ke da kashi 6.5 cikin 100; Daga cikin hanyoyin da take shigo da kayayyaki kuwa, Japan tana da kashi 21.7 cikin 100 na jimillar sayayyar intanet da kasar Sin ke shigo da kayayyaki daga ketare, yayin da Amurka ke da kashi 17.9 cikin 100. (Ibrahim)