Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da mutuwar tsohon Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), David Shikfu Parradang, tare da yin watsi da rahotannin cewa, ‘yan fashi ne suka kashe shi a Abuja.
A cewar mai magana da yawun ‘Yansandan reshen Abuja, Josephine Adeh, “Parradang ya je otal din Joy House da ke Abuja, a ranar 3 ga Maris, 2025, inda ya biya Naira 22,000 na kwana daya. Daga baya ya karbi bakuwa – mace, wacce ta fita daga ɗakin nasa da misalin karfe 4:00 na Asuba”.
- Kasafin Kuɗin 2025 Taswira Ce Ta ƙarfafa Tattalin Arziki Da Ci Gaban ƙasa – Ministan Yaɗa Labarai
- Arsenal Ta Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai
To sai dai bayan bin diddiginsa da wani abokinsa soja ya yi, ya gano cewa Parradang bai fita daga otal din ba, hakan ya sa shi zuwa otel din tare da sanar da ma’aikatan Otel din wanda hakan ya sa suka duba dakin, inda suka tarar da shi ya mutu akan kujera.
Rundunar ‘yansanda ta Durumi, ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da tattara bayanai, sannan ta mika gawar zuwa Asibitin kasa domin ci gaba da gudanar da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp