Jihar Xinjiang na daga cikin sassan kasar Sin da kafafen yada labarai na kasashen yamma suke son baza karairayi a kai. Idan ba a manta ba, a kimanin wata guda da ya wuce, sun ba da rahotanni game da wai “ana bautar da laburori” a gonakin noman auduga da tumatir na jihar Xinjiang, ga shi a kwanakin nan, sun karkata hankali ga barkonon jihar, inda wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma suka ce, wai kayayyakin barkonon da ake sayarwa a cikin kantunan Amurka da Burtaniya na kunshe da barkonon da ake nomawa a jihar Xinjiang, wadanda ya yiwu ake samarwa bisa aikin tilas, don haka sun yi kira ga kamfanonin kasashen yamma da su daina yin amfani da barkonon jihar Xinjiang.
Amma da gaske ne ana bautar da leburori a jihar Xinjiang?
A hakika, aiki ne ya kai ni jihar Xinjiang sau da dama. Birnin Wusu da ke arewacin jihar na daga cikin muhimman sassan da ke samar da tumatir a jihar, kuma na je birnin a watan Agustan bara, inda na gane ma idona yadda na’urorin tsinkar tumatir ke shan aiki a cikin gonakin tumatir. Mai gonar malam Zhang Tongquan ya ce min, fadin gonakinsa ya kai kimanin eka 133, kuma mutane hudu ne kawai ke kula da su, sabo da kusan na’urori ke dukkan ayyukan da ke shafar shuka tsiron tumatir da ma tsinkarsu. Ya ce, na’urar guda daya na iya tsinkar tumatir daga gonakin da fadinsu ya kai kimanin eka 6.7 cikin yini guda, wato aikin da kimanin leburori 150 suke yi ke nan, kuma hakan na iya rage kudin da yake biya wajen ayyukan tsinkar tumatir da kimanin kudin Sin Yuan miliyan daya.
Duk wanda ya taba shiga gonakin jihar Xinjiang ya san cewa, ko aikin noman auduga ko tumatir ko kuma barkono, kusan ana amfani da na’urori wajen gudanar da dukkan ayyukan. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, kimanin kaso 85% na ayyukan diban auduga a jihar Xinjiang, na’urori ne ke yi su, adadin da har ya kai 100% a akasarin sassan noman tumatir da kuma barkono. Gaskiya ita ce tushen ayyukan samar da rahotanni, ai su kafafen yada labarai da suka yada karairayi game da “aikin tilas a jihar Xinjiang” abin da su ke yi ba aikin jarida ba ne, a maimakon haka, tamkar suna tsara wasannin kwaikwayo ne, amma ko wannan aikin ma ba su cancanta ba, sabo da a jihar Xinjiang da ake yawan amfani da na’urori, ta yaya za a samu “aikin tilas”, ko suna nufin tilasta wa na’urori aiki ake yi?
To, amma me ya sa kafafen yada labarai na kasashen yamma ba su gaji da shafa wa jihar Xinjiang kashin kaza ba?
Bari mu dauki misali da auduga. Amurka na daga cikin muhimman sassan duniya da ke samar da auduga, wadda a baya ta kasance kasar da ta fi samar da auduga a duniya, sai dai kasar Sin ta maye gurbinta daga baya sakamakon yawan auduga masu inganci da ta samar, lamarin da ya zamanto barazana ga ayyukan samar da auduga a kasar da ma kasuwarta. Don haka, Amurka ta yi iyakacin kokarin dakile ayyukan samar da auduga a jihar Xinjiang, kasancewarta jihar da ta fi samar da auduga a kasar Sin. Hasali ma dai, ita Amurka ta saba da irin aiki, kasancewar ta taba sanya wa kasar Uzbekistan takunkumi ta fannin aikin samar da auduga bisa sunan wai “ana bautar da leburori yara a kasar”, kuma sanin kowa ne Uzbekistan kasa ce da ta shahara da noman auduga a tsakiyar Asiya.
Baya ga tattalin arziki, akwai kuma dalili na siyasa. Saurin bunkasuwar kasar Sin cikin ‘yan shekarun baya ta sa Amurka da wasu kasashen yamma matukar damuwa, don haka suke iyakacin kokarin neman dakile ci gabanta, kuma yadda suke sanya takunkumi a kan kayayyakin da ake samarwa a jihar Xinjiang na daga cikin matakan da suka dauka, a yunkurin lalata bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma a jihar, ta yadda za su cimma burinsu na yi wa kasar Sin tarnaki. Wani jami’in karamin ofishin jakadancin kasar Amurka da ke birnin Guangzhou na kudancin kasar Sin ya taba bayyana a fili cewa, “Dukkanmu na sane da cewa, Xinjiang ba ta da matsala, amma baza jita-jita game da matsalolin hakkin dan Adam a jihar Xinjiang mataki ne mai amfani, ta hakan za mu iya tsunduma kasar Sin cikin mawuyacin hali, kuma hakan zai amfanawa kasar Amurka.”
Auduga da tumatir da barkono da aka samar a jihar Xinjiang, kayayyaki masu inganci ne da suka yi suna har a fadin duniya, haka kuma ginshiki ne ga al’ummar jihar wajen samun kudin shiga. Amma yadda Amurka da kasashen yamma suke fakewa da sunan “kare hakkin dan Adam” wajen shafawa jihar Xinjiang kashin kaza, ya sa su rasa ayyukan yi, matakin da a hakika ya keta hakkin dan Adam na al’ummar jihar. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, ya zuwa karshen bara, sama da kamfanoni 100 a jihar sun daina ayyukansu sakamakon takunkumin da kasashen yamma suka sanya musu, kuma yawan mutanen da suke ayyukan da suka shafi sassaka da tufafi da abubuwan ado ya ragu da kimanin 28.6%.
Karya fure take ba ta ‘ya‘ya, in ji Bahaushe. Karairayin da ake kokarin yadawa game da Xinjiang ba za su kai ga canza gaskiyar yanayin da ake ciki na samun bunkasuwar tattalin arziki da walwalar rayuwar al’umma a jihar ba, haka kuma ba za su iya hana al’ummar jihar da ta kasar Sin baki daya ‘yancinsu na samun ci gaba da rayuwa mai walwala ba.