Akalla gwamnonin Nijeriya 13 ne ke jiran sauraron sakamakon karshe game da shari’o’in da suka biyo bayan zabukan da aka gudanar a jihohin kasar saboda makomar gwamnonin 13 ya ta’allaka ne kan sakamakon karar da suka shigar ko ake kalubalantar nasararsu a kotun koli.
Jihohin da abin ya shafa da kotun daukaka kara ke kalubalantar hukuncin da ‘yan takarar jam’iyyun adawa a zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga watan Maris sun hada da Jihar Kano da Plateau da Abia da Delta da Cross River da Rivers da Lagos da Sokoto da Nasarawa da Benue da Akwa Ibom da Taraba da kuma Jihar Bauchi.
- Kotu Ta Kori Karar Abba K. Yusuf Ta Tabbatar Da Hukuncin Kotun Zabe Da Ya Tabbatar Da Gawuna
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
Tawagar lauyoyin da ke kare wasu daga cikin bangarorin da abin ya shafa a jihohin sun shigar da kara gaban kotu a hukumance kamar yadda a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da wasu suka sha alwashin garzayawa kotun koli da ake sa ran za su gabatar a cikin makon nan don shigar da kara kotun.
Ana kuma sa ran babban Alkalin Alkalan Nijeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, zai ja kunnen alkalai don su fara sauraron kararrakin nan ba da dadewa ba.
Wannan shi ne mataki na karshe na kararrakin kujerun gwamnoni a jihohin da aka gudanar da zabe ranar 18 ga watan Maris.
Ma’ana, duk gwamnan da ya rasa shari’ar a kotun koli, ya bar ofishinsa kenan.
Wannan ya sha bamban da sakamakon da aka samu kan takaddamar zabe a kananan kotuna na kotun sauraren kararrakin zabe da kuma kotun daukaka kara da ta bai wa gwamnoni damar ci gaba da rike mukamansu ba tare da la’akari da ko sun ci ko sun fadi ba.
Matakin da kotun koli ta yanke kan kararrakin da suka taso daga hukuncin da kananan kotuna suka yanke kan zaben gwamnoni a kasar shi ne zai zama na karshe.
A tsakanin shekarar 1999 zuwa 2019, gwamnonin da ba su gaza takwas ba ne, wadanda aka kalubalanci zabensu a kotun koli, aka kuma tsige su daga mukamansu na gwamnoni.