Dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP na jihar Kano a 2023 Engr. Abba K. Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-gida ya yi alkawarin korar duk masu ba da shawara da ke aiki da hukumar tattara kudaden shiga na jihar idan har aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar.
Abba Gida-gida ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi yayin wani taron tattaunawa da ’yan takarar gwamna da kungiyoyin fararen hula suka shirya a Kano.
Ya ce masu ba wa gwamnatin Ganduje shawara kan tattara haraji a halin yanzu basu da wata kima, gwamnan ke amfani da su wajen karkatar da dukiyar jama’a zuwa aljihunan su. A cewarsa, sama da kashi 40 cikin 100 na kudaden shigar da ake samu ana baiwa masu bawa gwamnan shawara ne kan harkar tattara harajin jihar.
“Abin takaici ne duk da cewa ana zargin masu bada shawarar kan tattara harajin sun fi 20 amma Kano na fuskantar karancin kudaden shiga, wanda ya yi kasa da Kaduna da Sokoto.”
Dan takarar gwamnan a NNPP ya bayyana cewa zai karfafa ayyukan ma’aikatar tara kudaden shiga ta jihar Kano (KIRS) ta hanyar nazarin dokokin harajin da suka dace domin cika ka’idojin ma’aikatun tattara haraji na duniya.
‘Yan takara shida daga jam’iyyun NNPP, PRP, ADP, ADC, LP da SDP ne suka halarci zaman tattaunawar amma dan takarar jam’iyyar APC mai mulki kuma mataimakin gwamna na yanzu Nasiru Gawuna da na PDP Sadiq Aminu Wali ba su halarci taron ba.