Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya nada kwararren dan jaridar nan dan asalin Jihar Kano, Abdulaziz Abdulaziz, a matsayin mai magana da yawunsa.
Abdulaziz, dai yana cikin fitattun ‘yn jarida da suka kware wajen binciken kwakwaf da bankado badakala a Nijeriya.
- NSCDC Ta Yi Bankwana Da Jami’anta 7 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Kaduna
- Amurka, Kasar Da Ke Kawo Cikas Ga Kokarin Duniya Na Shawo Kan Annobar Covid-19
Lokacin da ya yi aiki da jaridar ‘Premium Times’, Abdulaziz, ya bankado cogen takardar kammala NYSC ta Kemi Adeyosun, abin da ya yi sanadin ajiye mukaminta na Ministar Kudi.
Daga bisani ya yi aiki a matsayin mataimakin Edita jaridar Daily Trust na tsawon shekara biyu, wanda a nan ma ya bankado sirrin manyan ‘yan bindiga da suka addabi wasu jihohin Arewacin Nijeriya; irin su Bello Turji da Auwalu Daudawa.
Abdulaziz ne ya yi rahoton nan na musamman da yamutsa hazo kan ayyukan yan ta’addan daji, inda ya zanta da ‘yan bindiga.
Abdulaziz, ya kuma yi aiki da jarifar Leadership sannan ya kuma yi aiki da jaridar Blueprint.
A wata sanarwa da ofishin yada labaran dan takarar shugaban kasar, ya fitar wadda take dauke da sa hannun Tunde Rahman, ta ce Abdulaziz zai taimaka wajen kawo sauye-sauye a harkokin yada labaran dan takarar shugaban kasar.