- Gwamnatin Tarayyar Ta Sanya Baki
- Jihar Kogi Ta Garzaya Kotu
- Al’ummar Yankin Na Cikin Dardar
- Rikicin Ya Shafi Farashin Siminti
- Wani Sabon Rikici Da BUA
A ranar 5 ga watan Oktoba ne wasu mahara dauke sun farmaki kamfanin siminti na Obajana (OCP) dake jihar Kogi, Kamfanin da mallakar rukunin kamfanonin Dangote (DIL), wanda aka kafa tun a 2002, wadannan maharan sun raunata wasu ma’aikatan Kamfanin tare da lalata wani bangaren inda kuma suka tilasta rufe shi.
Wanda sakamakon takaddamar da ta kunno kai tsakanin Rukunin Kamfanonin Dangote da gwamnatin jihar Kogi, ya jawo alakanta kitsa kai farmakin ga gwamnatin jihar, dangane da cece-kuce kan mallakar kamfanin.
Sannan dukanin wadannan bangarori guda ukun; su maharan, gwamnatin jihar, da rukunin kamfanonin Dangote, ana iya cewa rukunin kamfanonin Dangote ne kawai zai iya fayyace halin da kamfanin siminti ke ciki, wanda saboda haka ne rukunin kamfanonin Dangote ya yi tsayin daka cewa su suka mallaki kashi 100 bisa 100 na kamfanin tun a 2002.
Tare da bayyana dalilai da cewa sun karbi kamfanin Obajana Cement ne bisa kulla yarjejeniya da gwamnatin jihar.
Sakamakon wannan takaddamar wadda ta kunno kai tsakanin Kamfanin Siminti na Dangote dake Obajana a jihar Kogi, da gwamnatin jihar, ya ce ya fara aikinsa a shekarar 2002, wanda kuma ya kafu ne bisa tsari da dokokin Nijeriya, sabanin ikirarin gwamnatin jihar Kogi.
Har wala yau, Rukunin Kamfanonin Dangote ya sake bayyana cewa gwamnatin jihar Kogi ba ta da wani iko ko ruwa da tsaki a harkar gudanar da Kamfanin simintin da ke Obajana, tare da fayyace cewa, Kamfanin ya na biyan gwamnatin jihar Kogi haraji, da sauran hakkokin da suka rataya a wuyansa tun a shekarar 2007 lokacin da ya fara aikin samar da siminti.
Wadannan bayanai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mahukuntan kamfanin Dangote ya fitar dangane da takaddamar da ta jawo cece-kuce tsakanin sa da gwamnatin jihar Kogi.
Hakan ya zo ne saboda matakin da gwamnatin jihar ta dauka a ranar Larabar da ta gabata, inda ta yi amfani da yan daba wajen rufe masana’antar simintin Dangote da ke Obajana bisa zargin kkn biyan haraji da kuma mallakar hannun jari a kamfanin.
Hakan ne ya sa gwamnatin tarayya ta tsunduma bakinta a cikin rikicin, inda wasu masu ruwa da tsaki suka bukaci bangarorin biyu da su warware takaddamar cikin ruwan sanyi domin kada matakin ya karya karsashin masu zuba jari da kawo tangarda a harkokin tattalin arziki a kasar.
Sai dai Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote a wata sanarwar da ya fitar, wanda ya nuna fargabar masu ruwa da tsaki a kamfanin, musamman jawo asarar aiki ga ma’aikata sama da 22,000 wadanda ke cin abinci a Kamfanin su rasa ayyukan yi, kana da jefa dubban yan kwangila, dillalai, da makamantan su shiga mawuyacin halin tattalin arziki, sakamakon rufe Kamfanin simintin.
Ya yi nuni da cewa, a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen tattalin arziki, “Wanda kasarmu ke fuskanta a matsayinmu na yan kasa, mun yi imanin cewa dole ne a yi duk mai yiwuwa don ci gaba da tafiyar da tattalin arzikinmu yadda ya kamata, da samar da aikin yi ga jama’armu, sana’o’in dogaro da kai tare da kokari wajen dakile ayyukan tarzoma da na ta’addanci da masu daukar nauyinsa, wadanda mafi yawansu daga rashin aikin yi ne.
Wanda ko shakka babu rufe masana’antu babban cikas ne ga kasarmu.”
A cewar sanarwar, kamfanin Obajana na daya daga cikin muhimman harkokin tattalin arziki a Nijeriya, kasancewarsa daya daga cikin masu biyan haraji mai kauri, kuma daya daga cikin manyan kamfanonin da dubban masu zuba jari a Nijeriya da kasashen waje suka dogara dashi.
Kamfanin ya fayyace cewa filin da aka gina kamfanin simintin Obajana, mallakin Rukunin Kamfanonin Dangote ne a shekarar 2003.
“Saboda haka, da filin da aka gina kamfanin Obajana mallakin Rukunin Kamfanonin Dangote ne (Dangote Industries Limited), tun a shekarar 2003, kuma hakan ya zo ne bayan da ya mallaki hannun jari a Kamfanin simintin a shekarar 2002, biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla da Gwamnatin jihar Kogi, bisa dokar zuba jari ta jihar Kogi.
Kuma an bai wa Rukunin Kamfanonin Dangote Takaddun Mallaka har guda uku da sunan sa bayan biyan kudaden da suka wajaba da kuma biyan diyya ga masu filayen da Kamfanin yake.
Wanda a wata sanarwar da gamayyar kungiyoyin Kasuwanci masu zaman kansu (Organized Pribate Sector) ta fitar inda ta caccaki gwamnatin jihar Kogi dangane da matakin rufe kamfanin siminti na Obajana, mallakin rukunin kamfanonin Dangote, tare da bayyana yunkurin a matsayin karan-tsaye ga doka.
Kungiyar OPS ta bayyana wannan matsayar, a karkashin uwar kungiyoyin yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai tare da manoma ta kasa ta ‘National Association of Chambers of Commerce, Industries, Mines and Agriculture’ (NACCIMA), kungiyar yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) da kungiyar yan kasuwa da masana’antu ta Abuja (ACCI); a mabambantan sanarwoyi, tare da bayyana matakin gwamnatin jihar Kogi a matsayin rashin la’akari da dubban al’ummar da rufe kamfanin zai shafa kana da yadda zai jawowa jihar kaurin suna.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, hukumar gudanar da kamfanonin simintin Dangote sun sanar da jama’a; musamman abokanan kasuwancin su da sauran masu ruwa da tsaki game da farmakin da yan daba suka kai wa kamfanin simintin a Obajana da ke jihar Kogi a kwanakin baya, bisa zargin cewa da umarnin gwamnatin jihar aka kai wa kamfanin farmaki.
Kamfanin simintin ya kara da cewa ga dukkan alamu wasu yan daba a karkashin jagorancin wasu jami’an gwamnatin jihar sun dauki wannan matakin ne a wani kudurin da majalisar dokokin jihar Kogi ta yanke kan batun harajin da ya taso; bisa wani ikirarin da gwamnan jihar tayi wanda ya sabawa doka wajen daukar matakin rufe kamfanin, na zargin sayar da kamfanin ga rukunin kamfanonin Dangote.
Kamfanin simintin ya ce yan dabar sun rinka tilastawa ma’aikatan su da karfin tsiya ala-dole sai sun bar wajen, al’amarin da ya jawo sun harbe ma’aikatan kamfanin 27 tare da lalata wasu kadarorin masana’antar. Wanda hakan ya sanya jami’an tsaron kamfanin damke wasu daga cikin yan dabar domin zama shaida a gaban shari’a.
Darakta Janar na kungiyar NACCIMA, Olusola Obadimu ya ce, matsalolin da ke tsakanin kamfanin da jihar kan rikicin haraji bai kamata ya kai ga rufe kamfanin ba amma ya kamata a warware su cikin kwanciyar hankali da lumana. Tare da kira ga gwamnatin jihar Kogi ta bi hanyar taka tsantsan, ta gaggauta bude masana’antar domin a ci gaba da ayyukanta.
Gwamnatin jihar Kogi za ta garzaya kotu
Duk kokarin shawo kan wannan takaddama ya ci tura, saboda yadda aka kasa samun amincewar bangarorin guda biyu; wanda ko a ranar Jummu’ar da ta gabata an gudanar da zama na musamman tsakanin Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, dangane da kamfanin siminti na Obajana, saboda yadda kowane bangare yaki sauka daga matsayin sa.
Wanda sakamakon rashin samun daidaito, bayan duk kokarin masu ruwa da tsaki a takaddamar, inda aka tashi kowane bangare da dutsinsa a wuyan riga, al’amarin da ya jawo gwamnatins jihar Kogi ta yi barazanar kai rukunin kamfanonin Dangote kotu dangane da hakkin mallakar Kamfanin Siminti na Obajana.
Wannan ya fito ne daga bakin Kwamishinan yada labaru na jihar Kogi, Mista Kingsley Fanwo; a wata sanarwar manema labaru da ofishin sa ya fitar. Inda ya ce gwamnatin jihar za ta bi bayan hakkinta zuwa kotu har sai abin da hali yayi.
Mista Fanwo ya shaidar da cewa, gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan tuntubar masu ruwa da tsakin wanda Gwamnan jihar Yahaya Bello ya gudanar hadi da gamsassun hujjojin da suke dashi kan batun.
Ya ce, “Kuma dukkanin masu ruwa da tsakin sun goyi bayan a nausa zuwa kotu, saboda kare hakkin al’ummar Kogi tare da ya’yan mu masu zuwa nan gaba.”
“Har wala yau kuma, zamu kasance masu hada hannu da karfi wajen dawo da dukiyar al’ummar jihar Kogi kuma kareta da dawo da ita hannun masu ita ya zama wajibi.
Kuma wannan ita ce hanyar da gwamnati za ta bi, wanda gashi kuma mun fara, sannan kuma zamu dauki matakin shari’a har sai mun dangana da karshen tare da tsammanin yi mana adalci. Saboda babu wani bayanin da zai warware wannan takaddama.
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umurnin sake bude Kamfanin.
Majalisar tsaro ta Nijeriya ta bayar da umurnin sake bude Kamfanin Siminti na Obajana dake jihar Kogi. Yayin da ta tabbatar da cewa rufe Kamfanin ya zo ne sakamakon rashin fahimtar da ya taso tsakanin gwamnatin jihar da Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a wannan makon.
A zamanta na wannan makon, Majalisar tsaro ta kasa, a karkashin jagorancin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta bayar da umurnin sake bude Kamfanin sakamakon fahimatar junan da bangarorin suka cimma.
A lokacin da yake zantawa da manema labaru a Fadar Shugaban kasa, bayan kammala taron, Minista a Ma’aikatar Harkokin Yan-sandan Nijeriya, Alhaji Maigari Dingyadi, ya tabbatar da cewa bangarorin sun cimma matsaya kan batun tare da amincewa a bude Kamfanin wanda hakan zai zama mafita ga zaman lafiya a jihar.
Ya ce, “An cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Kogi da Kamfanin Siminti na Dangote da ke jihar Kogi dangane da bukatar sake bude masana’antar domin samun ingantaccen zaman lafiya a jihar.”
”Saboda yadda gwamnati ta ke kokari wajen ganin yan kasa sun samu ayyukan yi, sabanin jawo abubuwan da zasu haifar da rashin aikin yi ga jama’a.”
”Sannan kuma muna kyautta zaton dukan bangarorin da abin ya shafa zasu mutunta wannan yarjejeniya da aka cimma, tare da kawo abubuwan da zasu bayar da mafita a fahimci juna ga kowane bangare.”
Alhaji Dingyadi ya ce an yi nasarar cimma wannan matsayar ne a karkashin kulawar Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
A halin yanzu kuma wani sabon rikici ya sake barkewa a tsakanin gwamnatin Jihar Kogi da Kamfanin Siminti na BUA wadda ke karkashin jagorancin Alhaji AbdulSamad Rabiu, inda gwamnatin ta yi barazanar janye lasisin da ta ba kamfanin. Bayani ya nuna cewa, kamfanin ya ce, a shirye yake ya fita daga jihar in har gwamnatin ta janye lasisin da ta bata. Wannan ya sa wasu al’ummar jihar ke ganin akwai rashin hikima daga bangaren gwamnatin don kamar tana korar masu zuba jari ne wanda hakan kuma zai kai ga rasa aikin yi ga dimbin matasan jihar da ke aiki a kamfanonin