Hukumar Kula Da Yanayi ta Birtaniya, Met Office, ta fitar da gargadin samun mamakon ruwan sama da cida da iska mai karfi a fadin kasar, wanda zai zo da walkiya da tsawa.
Duk da cewar akwai yiwuwar faduwar tsawa, yana kuma da muhimmanci a san yadda za a kare kai lokacin da ake tsawa da walkiyar.
An bayyana cewa tsawa tana kashe mutum 24,000 duk shekara a fadin duniya, da karin mutum 240,000 da ke jikkata.
A duk mace-mace 50 da ake samu a duniya, to daya na faruwa ne a Brasil, wadda ita ce kasar da ke sahun gaba a duniya da tsawa ke yawan faduwa.
Yawancin mutane na sane da hanyoyin kare kai lokacin da ake tsawa, kamar gujewa tsayawa a karkashin bishiyoyi ko kuma kusa da tagogi da kaucewa amfani da wayoyin salula.
Amma kun san ya kamata kuma ku gujewa yin wanka ko wanke-wanke yayin da ake tsawa da walkiya?
Domin sanin me ya sa, da farko ya kamata ka san mece ce tsawa da yadda take aiki.
Abubuwa biyu ne ke haddasa samun tsawa: yanayin zafi da kuma iska me zafi da ke kadawa, wadanda ke tafiya dai-dai da lokacin bazara.
Yanayin zafi na kara yawan iska mai zafi, wadanda ke haduwa su janyo tsawa. Gajimare na dauke da miliyoyin digon ruwa da kankara, inda haduwarsu shi ne abin da ke janyo a samu afkuwar walkiya.
Digo-digon ruwa dake fitowa na haduwa da kankarar da ke zubowa, wanda ke sa su ba da wani martani na daban.
A lokacin da ake tsawa, gajimare na kasancewa kamar manya-manyan injuna na Ban de Graaf da ke sauyawa zuwa nau’ukan hasken lantarki domin rabuwa da gajimare.
Yayin da gajimare ke matsawa kusa da samaniya, suna samun karfi zuwa kasa, wanda hakan ne ke jawo a samu walkiya zuwa a kasa.
Walkiya hade da tsawa na kokarin daidaita yanayin, suna yin hakan ne ta hanyar aikewa zuwa yankuna. Wani bangare na yanayin na gamuwa da turjiya, inda tsawa ke saurin fadowa kan abubuwa da ke waje kamar karafuna da sauransu.
Shawarar da ta dace a irin wannan lokaci na tsawa ita ce: da zarar mutum ya ji alamar tsawa, to kawai ya shiga cikin daki.
Sai dai hakan ba yana nufin kwata-kwata mutum ya kubuta daga fadowar tsawa ba.
Akwai wasu ayyuka da mutane ke yi a waje wadanda ke da hadari kamar zama a waje lokacin da ake tsawa.
In ba wai mutum yana wanka a waje ko cikin ruwan sama ba, da wuya tsawa ta shafi mutumin.
Amma idan tsawa ta fada gidanka, hasken lantarki zai bi wajen zuwa kasa.
Abubuwa kamar wayoyi da karafuna ko kuma magudanan ruwa, na samar da saukakkiyar hanyar da wutar lantarki zai bi zuwa kasa.
Zai iya juyar da wannan wanka zuwa wani abu na tashin hankali. Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Amurka, ta umurci mutane da su guji shiga ruwa lokacin da ake tsawa har ma da wanke-wanke domin rage afkuwar hadari.
Akwai wasu hadura da ya kamata a kaucewa yayin da ake tsawa. Wani abu da mutane ke yi shi ne jingina da bango.
Bango ba wuri ne mai kyau na jingina ba idan an gina shi da karafa, wanda hakan zai jawo afkuwar walkiya da tsawa. Ya kamata kuma mutane su guji amfani da duk wata nau’ra da aka saka a caji kamar komfuta da talabijin da wanke-wanke saboda dukkan wadannan za su iya haddasa tsawa.
Abin da ya kamata mutane su yi shi ne, idan za ka ji alamar tsawa daga nesa, to tsawar tana kusa da inda kake, ko da kuwa babu ruwan sama.
Tsawa ta kan isa waje mai nisan kilomita 16 daga inda aka jiyo ta. Bayan jin alamar tsawa da rabin sa’a, to shi ne lokacin da ya kamata mutum ya shiga wankan da ya yi niyya. A yawan lokuta, walkiya hade da tsawa na farowa da kadan, inda ta baya ke fin ta farkon karfi.