Jarumi SANI ABUBAKAR, wanda aka fi sani da SANI INDOMIE da ya shafe kimanin shekara 20 a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ya bayyana babban dalilin da ya sa bai fuskanci kalubale sosai bay ayin da ya tsunduma harkar fim ciki har da wayon da ake wa sabbin shiga da ake wa lakabi da ‘kan-ta-waye’. Jarumin ya kuma yi tsokaci dangane da shirya fina-finai a baya da kuma na yanzu da sauran abubuwa da dama: Ga dai yadda tattaunawarsa tare da wakiliyarmu, RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko masu karatu za su so jin cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da shi.
Sunana Sani Abubakar, wanda aka fi sani da Sani Indomie.
Me ya sa ake kiranka da Sani Indomie, shin kanada alaka da Zainab Indomie ne ko kuwa suna ne ya zo daya?
Ko kadan ban da wata alaka da Zainab Indomie sai ta sana’a, ana kira na da Sani Indomie ne sabida na yi aiki a kamfanin indomie shekaru masu yawa.
Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Ni dan garin Kano ne kuma dan Gezawa, na fara karatun firamare a karamar hukumar Gezawa, ban karasa ba mahaifina dalilin aiki ya dawo cikin Kano, na dora karatuna a Kawon Mai Gari firamare, daga nan Tafarke Nassarawa, bayan na kammala daga nan dai Allah bai ba ni ikon ci gaba da karatu ba aka ci gaba da gwagwarmayar rayuwa.
Ya batun iyali fa akwai ko babu?
Ah! Iyali akwai, ina da Matata da kuma yarana guda uku, Allah ya ba ni.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood?
Na shiga masana’antar Kannywood saboda ina sa ran za ta zame mun sana’a ta biyu, dan lokacin dana shiga masana’atar Kannywood ina kamfanin Indomie, na shiga ne ina ganin za ta zame mani sana’a ta biyu a wancen lokacin, kuma abin da ya ja hankalina a wancen lokacin shi ne yadda na ga sana’ar tana da karfi, kuma ina da abokanai a ciki da suke sana’ar, toh gaskiya ta zame mun sana’a a lokacin, na shige ta da abin da na sa rai kuma ta nuna mun za ta yi mun in sha Allah.
Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?
Gwagwarmaya Alhamdu lillahi ana kan yi ba a daina ba, kuma an sha gwagwarmayar tun daga kan lokacin da ta zo ta zama sana’a daya tilo, ana ta gwagwarmaya an yi fadi – tashi, daga lokacin da ka zama sabo a cikin abu har zuwa lokacin da ka zo ka samu kwarewa a ciki da dadi da babu dadi ita aka iya kuma ita ake yi.
Toh ya batun kan ta waye da wasu suke fada an yi masu, shin ka ci karo da hakan ko kuwa?
Kamar yadda na yi miki bayani ni lokacin da na shiga masana’antar, na shige ta ne da kudina kamar yadda na ce na shiga ne matsayin sana’a ta biyu, dan haka ni ban ci karo da wadannan abubuwan ba; ko sai ka biya kudi ko sai ka debi shekaru, ko sai an yi maka kan ta waye, ban hadu da wannan kalubalen ba, tunda lokacin na shiga ne a matsayin furodusa.
Ya batun iyaye lokacin da ka fara sanar musu cewa kana son shiga cikin masana’antar, shin ka fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Toh! Alhamdu lillahi, gaskiyar magana lokacin da na fara sana’ar fim ban samu kalubale daga wajen iyayena ba, sakamakon yadda na je wa mahaifina a matsayin zan fara sana’ar fim, ya tambaye ni ya take? kuma nayi masa bayani ga yadda suke, kuma wadanda suke ciki sun yi masa bayani, dan haka ya gamsu da sana’ar, shiyasa ban samu matsala da shi ba sai addu’a da ya yi mun ya ce; “Allah ya bada nasara ya sa hanyar cin abincinka ce”.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara sana’ar fim?
Zan iya yin kamar a kalla shekara goma sha tara zuwa ashirin, ina masana’antar.
Wace rawa ka ke takawa a cikin masana’antar?
Ni furodusa ne mai shiryawa, sannan kuma jarumi ne ni, wannan rawar guda biyu ita ce wadda nake takawa.
Da wanne ka fara tsakanin fim da kuma shirya fim cikin masana’antar?
Na fara da shirya fim.
Wanne fim ka fara shiryawa, kuma ya karbuwar fim din ya kasance ga su masu kallon, sannan wanne irin kalubale ka fuskanta game da shirya fim, musamman wajen tattaro jaruman da kuma kudaden da ka kashe, shin kwalliya ta biya kudin sabulu ko ya abun ya kasance?
Alhamdu lillahi fim dina na farko sunansa ‘Sarewa’, a wancen lokacin wajen biyan kudin sallama, tunda ba ni ba ne furodusa, ni na yi furobaidin na kudi a wancen lokacin, akwai furodusan da ya yi mun Abdulhadi Awilo ne, sannan darakta na Mu’azzamu Dorayi, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Tunda a lokacin kaset ake bugawa na siyar, Abdulhadi shi ya yi ‘marketing’ ya saida mun kaset, aka buga kwali da sauransu aka sayar, kuma Alhamdu lillahi kwalliya ta biya kudin sabulu, tunda bayan na siyar da kwalin kafin na kara shirya wani fim an ja lokaci sai aka fara siyar da CD, ‘copyright’ na CD na siyar nan ma na samu. Gaskiya a fim dina na farko Alhamdu lillahi na dan samu babu laifi, wajen biyan jarumai kudi a wancen lokacin wanda ya fi kowanne karbar kudi ina ga Iyan Tama ne, kuma kudin bai wuce N25,000 ba a wancen lokacin.
Ya farkon fara fitowarka a fim ta kasance?
Farkon fara fitowa ta a fim, wani rol za a yi a cikin fim din da nayi, sai aka rasa wanda zai yi yadda ake so din wannan rol din, soyayya ce za a yi to, tunda an riga an saba bai zame mun wani abu me wahala ba, tunda kullum ina gani ana yi da sauransu, dan haka da aka ba ni wannan rol din bai zame mun wani abun wahala ba.
Daga lokacin da ka fara fim kawo yanzu ka yi fim sun kai kamar guda nawa?
[Dariya] Gaskiyar magana a nan tambayar babu amsa, ba zan iya sanin adadin fina-finan da na yi ba, suna da dai dama.
Ko za ka iya fada wa masu karatu kadan daga cikin fina-finan da ka shirya da kuma wadanda ka fito ciki?
Fina-finan da na fito kadan daga ciki na wancen zamanin akwai irin su; Karangiya, Hajiya Babba, Babban Direba, Musabbabi, hatta na zamanin nan ina ciki irin su; A duniya, na fito a cikin Labarina, Dadin Kowa, Ke Duniya, gaskiya na fito fina-finai da yawa. Sannan fina-finan dana shirya akwai irinsu; Babban Direba, Sarewa, Musabbabi, Gida Daya, Ibola, Kwamandan Mata, Bala Kafinta, fina-finai da dama wannan kadan ne daga cikin wanda na shirya.
Tsakanin shirya fim da kuma fitowa matsayin jarumi wanne ya fi wahala?
[Dariya] Ai ratarsu kamar daga Kano ne ka ce za ka tafi Kaduna a kafa, ai ratar shirya fim da fitowa a fim ba sa’anin juna ba ne. Mashiryin fim gaba daya nauyin kowa da kowa da aka tattara da wanda zai zo daga lokacin kirkirar labari har i-zuwa karshen fim, sai an gama komai da komai daga lokacin fa aka ce an sallami furodusa,
Wanne fim ne ya fi ba ka wahala wajen shiryawa da kuma fitowa matsayin jarumi?
Fim din da ya fi ba ni wahala wajen shiryawa shi ne; fim din Ibola, sabida shi a lokacin ana cikin abun ne kuma ake bukatar labarin gaba ki daya da yin sa da gamawa da fita aikinsa da rubuta labarinsa da komai bai wuce wata daya ba, dan haka gaskiya na sha wahala karkashin daraktana Ilyasu Abdulmumini Tantiri a wancen lokacin, da kuma jaruman, saboda shi ne fim da aka yi a gurguje aka gama shi. Amma fitowa a fim babu fim din da ya bani wahala irin Musabbabi, wanda shi kwanan nan ake nuna shi a tashar YouTube, sabida yanayin karaktar da na yi a ciki da sai ka lankwasa ba ki zuwa wani harshe wanda ba naka ba.
Da yawan wasu mutanen na ganin kamar fara fim da kammala shi cikin kankanin lokaci, na janyo rashin tsara fim yadda ya kamata kamar yadda sauran fina-finan waje suke daukar lokaci kafin su kammala shirya fim, me za ka ce a kan hakan?
Eh! Toh, abun haka yake amma sanin kowa shi ne; idan fim ya samu ma’aikata wadatattu kamar yadda shi fim din Ibola ya samu, ina ga zai kammala kuma zai ba da abin da ake so dan an wadata mana ma’aikata, duk abin da ake sa mutum daya an saka mana biyu zuwa uku, hatta wadanda suka yi rubutun ba mutum daya ba ne kamar yadda muka saba, mutane ne suka hadu suka rubuta labarin, dan haka ba a samu irin wannan tangardar ba.