Babban abin da ke ba ni haushi da halin mata shi ne, sun mayar da namiji wani BOLA in da za su yada dattinsu.
Ba mutuntawa, sai tsabar korafi da nuna yawan bukatu.
- Burin Bai Wa Jama’a Shawarwari Ya Sa Na Fara Waka – Jamilu JEY BOY
- Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Yake
Kudin kunshi, Kudin bleaching, Kudin kitso, Kudin anko, Kudin kati, Kudin Karya, Kudin cefane.
To, Allah Na kallon mu dai mata. Me ya sa na ce haka?
Ba a ce ka da namiji ya yi wa matar shi gata ba. (Haka Allah Ke So) Har lada da farinciki zai samu. Amma yawancin matan yanzu babu tausayi a zukatansu, sai son kai. Kawai a basu kudi. Wai ba sa ganin kiman namiji sai yana sauke hakkinsu.
Idan bai samu ba, ya zama azzalumi wai…To amma ya samun nashi yake?
Amma ai ana ganin aikin namiji a yanayin matan senatoci, gwamnoni, da sauran masu kudi…yadda mata ke walawa suna kashe kudi.
Sai a ce namiji MUGU ne kawai don ya kasa wasu abubuwan da ake jira ya yi? Ba tausayi? Ba hankurin jira?
Ke mai korafi ba zaki nema ba? Tabbas akwai miyagun maza amma sam ba su da yawa…kururuta YAWANSU ake.
Daga Uwa Aishatu Gidado Idris
IPOH: Yaro Ya Mun Gorin Hausa
Yaro ke nan. Hausa yare daya ne cikin yarukan da nake ji ko nake rubutu da su. In ka ga na yi rubutu da Hausa saboda Hausawa ne (ba yan IPOH) su fahimce ni. Haka kowane marubuci yake yi.
Rubutuna 90% da Turanci nake yi. Ina amfani da Turanci idan Nijeriya nake wa magana. Ina amfani da Hausa idan Arewa kawai na fuskanta. Idan ya kama in ida sako da hillanci sai in yi, mashaallah, don akwai Fulanin da ba su ma san akwai Hausa a duniya ba. Ka yi yawon duniya ka gani. Na fara da Larabci saboda malamai kuma zan habaka shi.
Maganganu irin wadannan za su kawo ma Hausa cibaya ne ba cigaba ba. Alal hakika daba wa kai wuka ne. Idan IPOH Hausa za su yi gori, wadanda za su yi wa gorin suna da yawa. A yau, wadanda ke magana da Hausa sun fi asalin Hausawa yawa. Haka kuma wadanda ke gidajen rediyo, da makarantu kanana da manya, da hukumomin gwamnati inda ake hulda, ko ake yin manufofi (policies) da suke kawo cigaba ga Hausa fiye da kowane harshe. Idan IPOH suka cigaba da gori, anya akwai hikima kuwa?
Akasarin yarukan da suka bunkasa za ka samu wadanda ba yan kabilarsu ba sun taimaka gaya wajen cigabansu. Malaman Larabci da Swahili da Fulatanci za su ba mu misalai da yawa. Hausa ma haka.
Ba zan iya kirga mutanen da ba Hausawa ba da suka taimaka ga daga harshen Hausa, tun daga shi kansa uban gayya Shehu Usumanu Danfodio zuwa manazarta, marubuta, masharhanta, mawaka, malamai, dss, na yau. Kan da za a zayyana maka gudummawar da Fodiyawa suka ba harshen Hausa da za ka sha mamaki. Amma ka kusanci malaman Hausa ka sha labari.
Haka kuma za a cigaba ko yan IPOH ba sa so.
Hattara! Allah ya yi hani da gori. Hausa ni’ima ce gare mu duka. Allah ya ba mu ita ta zame mana zare na dinke Arewa, musulminmu da kiristanmu. Duk lokacin da ka yi magana da Hausa, kana taimaka wa wajen bunkasa Hausa ne. Haka in ka yi rubutu da shi, ko wa’azi, ko magana a gidan rediyo, ko waka, ko wake, dss. Ba gori za a maka ba. Jinjina maka ya kamata a yi.
Duk wadanda suka cigaba, idan suka ji kana harshensu, son ka da girmamaka suke yi. Banda yan IPOH da ke son mai da Hausa baya. Su gori za su maka kamar yanda za ka ji su a comments yanzu nan a kasa.
Mu kam tsakaninmu da Hausa, sai kirari:
Fa Hausa zare ne na dinke mutane Arewa gaba dai fa jigonmu Hausa.
Gyara kawai da zan yi wa yaron shi ne Hausa ba hanyar cin abincina ba ce. Wani ma ya ce sun ba ni kasa na zauna. Nan ma, ba a kasar Hausa nake ba. Hausa harshe ne (Lingua Franca) na yankinmu na Arewa, mallakarmu duka.
Daga Dr. Aliyu U. Tilde
Gajeren Labari Don Nishadi: “Ni Ba’ankare Ne”
Wani mai wasa da kunami duhu ne na tsaka da kewaye a tsakanin mutane a Kasuwa kamar yadda suka saba, sai ya ji a na tsegumin wani makaho da ya zo gittawa yana bara cewa, kar yake da idanunsa. Kawai dai yana kanne su ne don jarabar son yin bara da son banza!.
Ko da ya ji haka, nan da nan sai ya dirfafi wannan makaho yana mai cewa; “Malam Makaho ga sadaka”.
Ko mai karatu kuwa ya san da cewa, wasu manyan kunami uku ya za6o tare da mika su ga wannan Makaho a matsayin sadaka!. Ko da wannan makahon karya ya waigo cikin hanzari, sai dai ya yi kwalli ne da bakaken kunami ne uku duhu. Nan da nan sai ya kada baki ya ce:
“Daga jin muryarka na fahimci kai ba mumini ne ba, saboda haka ba na karbar sadaka a hannun fajiri wanda ba ya ji, ya ki ji, ba ya gani, ya ki gani. Wanda ba ya yarda a zalunce shi ya bar wa Allah”
Sai jama’ar da ke wannan waje suka bushe da ihu. Su da kansu, sun fahimci Mati Makahon karya tuni ya kai gano cewa an miko masa kunami ne ba sahihiyar sadaka ba. Sai wannan mai wasa da Kunami ya wilkita idanunsa irin na mai yin sigina, kana ya amsawa makahon boge da cewa:
“Haba Malam Makaho, a ina ne aka ce sai a wajen Mumini ne kadai za a amshi sadaka?”.
Makaho; “Ba sai na fada ba, amma dai ai ka san ilmi kogi ne koh. Wai ma tukuna, kai dan wace Mazhaba ne?”.
Mai Kunami; “Ni Ba-malike ne. Kai fa?”.
“Ni Ba’ankare ne, ka ga ma tafiyata, ba na son yawan jidali cikin batun lislama. Ka rike sadakarka, Allah Ya amfana maka caaan”.
Nan da nan Mai Kunami ya yi tamau da cunar rigar makahon karya. Sai jikin Makaho ya hau bari yana mai cewa;
“Bawan Allah, ai ba sai ta kai mu ga wani rikici ba, idan ka gaiyace ni zuwa ga Malikiyyar sai na shiga. Ni dai fatana don Allah ka bar ni na tafi”
Mai Kunami; “Ai ni babban fatana shi ne ka karbi wannan sadaka tawa cikin ib a sanyi, ba tare da wani yunkurin kafirta ib a”.
Mai Kunami na magana tare da jefa hannu cikin kwanon da ke dauke da kunami, nan fa Makahon karya yai kukan kura, ya tankwabe hannun mai kunami. Ya saki sandar da ke hannunsa tare da tsallake wani wangalelen kwalbati, ya cika wando nai da iska.
Ganin haka, sai jama’ar da ba su yi masa cikakken sani ba, suka rika yin salallami tare da mamakin ashe Mati ba makahon gaskiya ne ba.
Mukhtar Anwar, ya rubuto daga Kano