• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abinci Shi Ne Tushen Rayuwa

byCMG Hausa
3 years ago

MDD da hukumomin kasa da kasa su kan fito da jerin tsare-tsare da manufofi, baya ga wasu ranaku da ake kebewa a duk shekara, don nazartar irin nasarori da ma akasin haka da bangaren aikin samar da abinci a duniya ke fuskanta. Sai dai annobar COVID-19 da ke ci gaba da addabar sassan duniya, ta haifar da illoli da sauran matsaloli ga bangaren samar da abinci a duniya, inda alkaluma ke nuna cewa, kusan kashi 10% na yawan al’ummar duniya na fuskantar yunwa.

Sai dai yayin da wasu kasashe ke nuna halin ko’in kula kan wannan lamari, ita kuwa kasar Sin a matsayinta na babbar kasa mai tasowa, wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, wajen ganin duniya ta amfana da duk wata irin kwarewa da fasahohinta, musamman kasashe masu tasowa, baya ga taimakawa kasashe masu tasowa, wajen inganta ayyukansu na noma ta hanyoyi daban daban.

Kasashen Afirka da dama, kamar Najeriya sun amfana da irin fasahohin noma da ma irin shinkafa mai inganci daga kasar Sin, matakan da suka taimaka matuka wajen kara yawan shinkafar da ake nomawa a irin wadannan kasashe fiye da shekarun baya.

Bayanai na nuna cewa, daga lokacin da aka kaddamar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa karkashin hukumar samar da abinci da gona ta MDD wato FAO, a shekarar 1996, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta tura masana ayyukan gona da injiniyoyi kusan 1100 zuwa kasashe sama da guda 40 na nahiyar Afrika, da Asiya, da kudancin Pacific, da yankin Caribbean da sauran sassan duniya. Abin da ya kara nuna muhimmancin da kasar Sin ke bayarwa ga batun samar da abinci, kasancewarsa tushen rayuwa, sabanin yadda wasu kasashe ke buya abinci, inda suke amfani da shi a matsayin makami na haifar da yunwa a duniya.

Karkashin kulawar hukumar FAO, kwararrun kasar Sin sun yi aiki tukuru wajen daga matsayin fasahohin ayyukan noma sama da 1000 a kasashe masu yawa a fannoni daban daban na aikin gona, da kiwon dabbobi da halittun ruwa, da noman rani, da kuma sarrafa kayan amfanin gona, lamarin da ya taimaka wajen bunkasa karuwar samar da irin shuka a gonaki daga kaso mai tarin yawa. Haka kuma kusan manoma 100,000 a kasashen duniya ne suka samu irin wannan horo daga masanan na kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

A gabar da duniya ke fama da tasirin annobar COVID-19, baya ga matsaloli na sauyin yanayi da shi ma ke yiwa bangaren aikin gona illa ta wasu fannoni. Sai dai kamar kullum, bikin magaji ba ya hana na magajiya, ma’ana hakan ba zai hana masu ruwa sa tsaki daukar matakan da suka dace na ganin an wadata duniya da abinci ba.

Bayanai na nuna cewa, akwai tarin jama’a a sassan duniya dake fama da yunwa sakamakon wasu matsaloli ko dalilai ko matakan kashin kai da wasu kasashen yamma suka dauka. Matakai da tsare-tsare da kasar Sin ke bijiro da su karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, sun taimaka matuka wajen kara samar da abinci da ma dabarun noma kala-kala a sassan nahiyar. Masana na cewa, kasashen Afrika za su iya amfani da huldar dake tsakanin Sin da nahiyar, wajen kawo gagarumin sauyi a tsarin aikin gona, da magance yunwa, da karancin sinadarai masu gina jiki, da kuma habaka tattalin arzikin mazauna karkara.

A cewar shugaba Xi Jinping na kasar Sin, dalilin da ya sa JKS mai mulkin kasar ke samun cikakken goyon baya daga al’ummar kasar shi ne, tana tsayawa kan kokarin tabbatar da ingancin rayuwar jama’a, musamman manoma.

Wannan na nuna cewa, idan har ana son wadatar da kasa da abinci, ya kamata mahukunta su taimakawa manoma don su samu karin kudin shiga, da raya kauyuka, da kuma ci gaba da zamanintar da aikin gona. Don haka, abinci shi ne tushen rayuwa, amma ba makami na siyasa ba. (Ibrahim Yaya daga Beijing, China)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Tattaunawa: Hulda Da Kasar Sin Muhimmin Ginshiki Ne Ga Ajandar Samar Da Abinci A Afrika

Tattaunawa: Hulda Da Kasar Sin Muhimmin Ginshiki Ne Ga Ajandar Samar Da Abinci A Afrika

LABARAI MASU NASABA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version